INGANTACCIYAR HANYAR YIN MU'AMALA DA MUTANE
Addinin Musulunci kamar yadda muka sani addini ne kammalalle, kuma addini ne wanda ya koyar damu dukkan yadda zamu rayu a wannan duniyar ta hanyar da zamu yi aiki acikinta sannan mu samu sakamako ranar gobe kiyama.
Hanyar Yin Mu'amala da Mutane
Al-Kur'ani da sunnah sun zo mana da bayanai daban-daban. Amma a takaicen takaitawa na takaita wannan dan rubutun ne domin tunatar da 'Yan-uwa game da HANYAR MU'AMALA DA MUTANE.
Wajibi ne mutum yasan hanyoyin da zai ringa mu'alantar 'Yan-uwa, domin ya kiyaye fadawa cikin hakkokin su kasancewar idan kayi wasa da hakkin mutane ta hanyar da bata dace ba toh hakika zaka yi dana sani, domin ALLAH (SWT) baya yafe Hakkin da ke tsakanin wani da wani face sai idan su suka yafi junan su.
Hanyar Yin Mu'amala da Mutane
Da wannan nake tunatar da 'Yan-uwa wasiyoyi guda tara
(9) acikin suratul Hujurat dan kula dasu wajen mu'amala:
1. Bincike idan anzo maka da wani labari.
2. Sulhu a tsakanin mutane.
3. Yin adalci yayin yanke ko wani hukunci.
4. Kada ka ringa yiwa mutane izgilanci.
5. Kada ka aibata wani.
6. Kada ka ringa yiwa mutane Lakabi da sunayen banza.
7. Ka guji mummunan zato.
8. Kada ka ringa bibiyar wani kan dole sai ka gano aibinsa.
9. Kada ka ringa giban mutane (wato gulma). Duk wanda ya kiyaye wadannan abubuwan a cikin mu'amalar sa da mutane, toh hakika zai rayu dasu cikin fahimtar juna da walwala.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku