Ka Fara Bincikar Kanka, Ma'aikatanka Da Ministocinka Da Gwamnoni Na Buhari Kafin Ka Ce Za Ka Yi Wani Bincike; Cewar Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Nijeriya
..... Ya zama dole ka fara titsiye kanka da ma'aikatanka tare da ministocin da ka baiwa mukamai har da gwamoninka.
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya, kamar yadda ta saba, ta bayyana damuwarta game da karuwar rashin tabbas da wasu masu tayar da kayar baya ke kokarin haifarwa a kasar yayin da ake kokarin mika mulki a watan Mayun 2023 zuwa sabuwar gwamnatin da aka zaba ta hanyar tsarin zabe na dimokiradiyya a watan Fabrairun 2023.
Mun lura da cewa wadannan abubuwan sun yi daban-daban daga aiyukan babbar kungiyar tsaro ta kasa, DSS, babban kwamandan sojoji da rundunar ‘yan sandan Najeriya ba tare da an samar da wasu matakan da za a dauka don dakile su ba.
Kungiyar ta CNG ta kuma damu da rahotannin da ke cewa wasu manyan jami’an gwamnatin mai barin gado na shirin barin kasar gabanin mika mulki, ko shakka babu a wani yunkuri na yin rufa-rufa a kan rashin da’ar da suka yi a ofis da kuma gudun kada a gurfanar da su a gaban kuliya. Mun damu matuka da rahotannin da ke cewa Godwin Emefiele wanda ya rike daya daga cikin manyan ofisoshi a kasar nan a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya a tsawon shekarun da Najeriya ta yi fama da tabarbarewar tattalin arziki da tabarbarewar kudi, na cikin wadanda ke shirin yin gudun hijira zuwa kasashen waje.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku