Illar ‘Tiktok’ Ga ’Ya Mace !
Daga Ibrahim Y. Ibrahim
Yau she Surar jikin ki ya zama mahaɗin isar da saƙo? Miye Amfanin isar da saƙon da ze zama sanadiyar sa wasu sun saɓa ma Allah? Kisan cewa a matsayin ki na ’Ya mace Surar jikinki ba abin tallatawa bane a cikin gidanku bare shafukan ‘Social Media’ wurin da bashi tsafta ko kaɗan‚ ke kuma a wurin ne zaki yada Zango domin tallata Surar jikinki domin samun ‘Followers’ a matsayin ki na halitta mai tsafta? Kinsan cewa wannan Surar naki fitinace da take fitininar da al’umma in a tallatashi a Muhallin da bai dace ba? Kinsan adadin mutanen da suke yabon Surar jikinki a kafar ‘Tiktok’ in ki sake ‘Video’ ? Kinsan adadin mutanen da suke kallon ‘Vedion’ ki domin yana kwantar musu da sha’awa?
Magana nake da Matan dasu fitar da kansu daga cikin jerin mata‚ domin ko wata Halittar da ba mutum ba‚ basa aikata Irin wannan aikin domin basu da Hankali‚ ke kuma kina da Hankali kinsan abu me kyau kinsan mare kyau‚ kinga ashe kin zama tsaiɗaniyar kanki tunda kin hana kanki bin umurnin Allah da yace ki kiyaye tsaraicin ki ga mutanen da basu da hurumi a kanki. Duk macen da ta mayar da tsaraicinta abin Tallatashi a Duniya domin ta samu abin Duniya tayi suna a Duniya ta mutu ta barshi a Duniya‚ ta daina alaƙanta kanta da sunan ’Ya mace‚ domin wannan ba siffan Mata na gari bane‚ muddin taci gaba da kiran kanta da ’Ya mace‚ to ta tanaji abin da zata faɗa ma Allah gobe ƙiyama‚ amma sam ta daina kiran kanta da sunan ’Ya mace tasan sunan da zata kira kanta.
Wani irin muhimmiyar saƙo ake son Isarwa ga wanda akeso ya isa da har sai kin haɗa saƙon da surar jikinki da ado masu jan hankalin? Kin samu ‘Bgraound’ me kyau kin hau ‘Tiktok’ kina ‘Maming’ ɗin waƙa harda rausayawa wani saƙo ki isar? Ba ina nufin yin ‘Tiktok’ ga ’Ya Mace babu kyau bane‚ zamani ne yazo dashi se ayi amfani da shi ta hanyar daya dace daidai da shari'a‚ kuma a dena sanya ‘Vedio’ ɗin da zaija hankali. ba mamaki ma tanan Allah ta'ala zai Sanyamu cikin ragamar sa amin.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku