A cikin rayuwa sai kayi a hankali, idan ba haka ba wasu mutanen da kake zaune dasu a garin ku ko Unguwar ku zasu rude ka ko su yaudare ka ba tare da ka sani ba. A dai dai lokacin da kake yin wata Sana'a ko wani aikin da kake samun Kudi, akan kai lokacin da wasu zasu dinga nuna maka ai ka kai ka sayi Mota, ka kai matsayin da zaka dinga sanya Tufafi masu tsada, bai dace kamar ka ace baka da Gida iri kaza ba.
Idan ka rudu da wadannan kalaman zaka fada cikin Rami me zurfin da fitowa daga cikin sa zai maka wahala, kai kadai kasan matsalar dake gaban ka, kada ka yarda wanda bai san matsalar ka ba ya nuna maka ai ka dace ka mallaki kaza.
Tabbas zaka ga kana samun Kudi kam, toh amma kana daukan nauyin mutane da dama a karkashin ka, kana ciyar da mutane akalla Goma, amma wani wanda baya ciyar da ko mutum 'daya zai zo yace maka bai dace ka zauna baka da mota ko gidan Miliyan goma ba
Kai kuma kasan kana taimakon Kannen ka dake karatu ko 'yan uwan ka mata dake gidan Miji, ga iyaye ga iyalin ka. Shi kuma wani zai ga toh idan da shine yake samun Naira dubu 100,000 a duk Wata irin yadda kake samu ai da yanzu ya sayi Mota, da yayi kaza da kaza, shi yadda yake ganin ka a zahiri baya ganin matsaloli da nauyin dake gaban ka.
Shi dai yasan kana samun Kudi amma bai san irin 'kura da Hayakin dake kanka ba.
Kada ka biyewa ma wadanda Kudaden su suke karewa a Shaddoji da Gezner da manyan Wayoyi, idan kabi wannan sahun toh zaka kai lokacin da baza ka iya mallakar komai naka ya zauna ba.
Akwai wani abu me rudan wasu a yanzu a wannan zamanin namu, shine: Wayoyi sunyi yawa, Camera ta daukar Hotuna suna da yawa, zaka ga mutane suna ta daukan Hotuna masu kyau, ga Riga me tsada, ga Hula me Tsada, ga Fatar jikin su yayi kyau, wannan abun sai ya Rudi mutane suga cewa suma sai sun mallaki irin wannan tufafin don suma suyi hoto me kyau me haske.
Kayi hakuri ka gama da Matsalolin dake tare da kai, daga baya zaka zo kayi ado kayi duk irin Kwalliyar da kake so.
Sau da yawa zaka ga matasa suna gasar Riguna, Huluna, Takalma da Wayoyi, idan kaji kudaden su sai ka rike baki, wadannan kudaden da ace wata harkar Kudi zai je ya zuba su da sun fi zama alkhairi.
Babban sakon dai shine mu cire girman Kai, kar ka damu da wai an saba ganin ka da Riga kala daya, ko Takalma iri daya, ko kuma ace wane fa tun shekaru kaza yake sanya rigar nan, kar ka damu da wannan kai dai ka fuskanci matsalar dake gaban ka kawai, matsalar da su masu yin maganar basu santa ba, ko sun sani babu abinda za suyi Maka akai.
Ka kalli kanka, yanzu kana Makaranta, kana samun Kudi, toh sai kayi kaffa kaffa da kashe kudade babu gaira babu dalili. Ko kuma yanzu kana da aure a gaban ka, zaka gina gida, ko zaka kama Haya, zaka yi Sadaki da Kayan Lefe, toh ka watsar da wadancan kalaman da wasu suke yi ai ya kamata ace kana Saka Riguna iri kaza.
Kada ka 'dorawa kanka wai kai sai an ganka da abu kaza alhali akwai kalubale a gaban ka, kada kaje ka kashe kudi akan abinda ba lallai ne ba, ka kyale abinda shine lallai, idan lokacin abun yazo a barka da fargaba da tashin hankali saboda ka batar da kudade akan abinda bai kamata ka batar ba.
Allah yasa mu dace.....
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku