Idan Aure Yana Zama Wajibi, Ya Wajaba Akan Hajiya Layla Ali Othman

KDK Hausa





Shugaban kungiyar malaman falaki na Nigeria Sheikh Habibi Abdallah Assufiyyu ya shawarci Hajiya Lailah Aliyu Uthman tare da tunatar da ita, cewa idan aure yana Zama Wajibi akan mutane musamman mace, to lallai babu shakka yazama wajibi akanta, domin kuwa ita ba Dutse bace, kada wayewa da ra'ayin boko su sanyaki tauyewa rayuwarki hakkin kanki da kanki nayin aure, domin aure babbar ni'ima ce.   

Al Sheikh Asufiyyu ya cigaba da cewa kina kokarin hana kanki wani sashi na jin dadin duniya wajen fifita wani tunani da kike ganin wayewa ce ko ra'ayi, musamman kedin da yazama kintaba aure, babu wani abu da baki sani ba akansa, domin baki isa kice babu wani natsuwa da ake samu acikinsa wacce kuma babu inda tadace asameta idan ba acikin aure ba, wannan dalilin kadai ya isa yazama dalili kan cewa zamar mace kamar ke babu aure yana cike da manyan kalubale, balle maganar iya zama batare da ketare iyakar ubangiji ma bata taso ba.

 Har sai yaushe ne zaki gane cewa cutar da kaine hana kai abunda kai ke bukata saboda rarraunar ra'ayi ko tunani? A ce kamar ke kina kaucewa aure ta inda babban jin dadin duniya ya karkata, bayan tarin tsira da rufin asiri da yake cikinsa. 

A wani hira da Jaridar BBC yayi da Hajia Lailah Aliyu Uthman, yasa ta bayyana ababuwa da suka shafi yadda tadauki rayuwa a duniya tare gudanar da nata rayuwar bisa wayewar da tunaninta yabata, inda take ganin zata iya rayuwa babu aure matukar zata kiyaye iyakokin ubangiji, hakan ya inganta amma : 

A daidai wannan gabar nakeso najawo hankalinki zuwa kan abubuwan da suka dace, sabanin yadda ke kika dauki naki rayuwar ; da farko dai al'umma sun dade suna kyautata miki zato akan abunda ya shafi ilimi, sanin yakamata da kuma natsuwa abisa Kamala data bayyana atare dake, a yayinda babu wanda yasan hakikanin dalilin dayasa bakida aure ayanzu, saidai bayan tattaunawar da kikayi da jaridar BBC, ke yanzu wani wayewa ce ko ra'ayi zai hanaki dawwama cikin morewa dadin dake cikin aure koda cikin lallabawa ce ? 

 Yakamata ace kigane cewa shi rayuwar aure ana daukarshi ibada ne koda cikin lallabawa ne, domin yana cike da kare martabar ah'linta tare da zama garkuwa ga dukkan wanda ya jibinceshi, musamman diya mace, nasan kinsan da wannan, Amma mai yahanaki amfanuwa dashi amatsayin ilimi ? Lallai akwai ganganci tun na yaranta atare dake, ina mai zaburar dake daga saita tunani adaidai wannan gabar, domin lokaci bai kure maki ba...

A wani bangaren kuma ba dalili bane wanda ya inganta cewa mace ta nemi miji ya saketa da gangar matukar yana iya kiyaye mafi galibin hakkokinta akansa, domin munji maluma suna fadar mana sakamakon matar dake neman saki daga wajen mijinta dakanta alhanin shi mijin yana sonta, baki tsoron afkawa cikin fushin Allah a kokarin ki na gujewa wata shubuha da kike ganin yana iya zama sabawa Allah ? 

 Wani tunanin yana fada mini cewa kamar kinajin dadin yadda matasa ke gasar bayyana sakon soyayyar su agareki akafafen sada zumunta cikin salo mabam-banta, wanda nasan da ace ya bayyana cewa kinada aure babu wani wanda zai kwadaitu da soyayyar ki arai haryazo yana magantuwa a kafar sadarwa. Saidai burgewa kawai akan salon yadda kike rayuwa da zai cigaba da wanzuwa a zukatan mabiya shafukanki idan kin cigaba da sada zumunta. Sannan nasan cewa ba'a iyawa mutane amma akwana atashi mutumcin ki zai iya gauraya da kasa idan baki kiyaye ba, a irin wannan salo naki na gujewa aure sunnan manzon tsira ( saw). Allah ya kiyaye ! 

Lallai yakamata kisani babu wani dadi a duniya da ya wuce samun mace saliha acikin zaman aure, kamar yadda samun namiji salihi yake awajen mace, babban Addua ta agareki akarshe wacce kuma shawara ce shine ki sauya tunani tareda samun mijin aure daga cikin mane manki, dole amatakin da kike yanzu yazama kinada wasu manyan bukatu wanda kudi bazai biya maki ba saidai aure. Saboda haka kiyi aure ki more arzikin da Allah yabaki. 

Allah yasa sakona ya isa gareki. Kuma Allah yabaki daman yin tunani akan dukkan abunda nafada. Amin.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku