Daga : Dr Jamilu zarewa
Assalamu alaykum. Tambaya malam saurayi da budurwane shaiɗan yashiga tsakaninsu har yakaiga saurayin ya tsotsi nonon budurwan har saida ruwa ya fito. Hakan yafaru ba so ɗaya ba, ba biyu ba amma bata taɓa ganin ruwan ba sai ranar. To mallam yaya hukuncin aurensu, ya halatta suyi auren? Kuma minene hukuncin shan Ruwan da yayi?
Wa’alaykumussalam, To É—an’uwa wannan abin da suka aikata mummuna ne, Tun da Allah ya haramta taÉ“a jikin matar da ba ka aura ba, kuma kofa ce da za ta kai zuwa zina, idan mutum ya tsotsi nonon mace bayan ya girma Amma babu ruwa a ciki, wannan ba zai haramta musu aure ba, amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi saÉ“anin akan hakan zuwa maganganu guda biyu :
1. Ya halatta su angunce, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu, saboda faÉ—in Annabi ï·º “Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa” , Bukhari lamba ta : 5102,
Ma’ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.
2. Yana haramta aure, saboda ko da yaushe mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi ï·º ya umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta agare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure.
Zancen da ya fi karfi shi ne nonon da mutum ya sha bayan ya girma ba ya haramta aure a tsakaninsa da matar da ta ba shi.
Don neman Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67.
Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas zai kiyaye shi, Wanda ya saɓa masa zai same shi a madakata.
Allah ne mafi sani.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku