Daga A'ishatu Adamu Saraki
Hausa ko Fulani, zage- zage da aibata juna babu inda zai kai mu duka! Shirme ne kawai da shiririta daga wadanda suke yi daga dukkan bangarorin biyu!
Yanzu a ce kana Bafulatani ka zagi Bahaushe, ko kai Bahaushe ne ka zagi Bafulatani, meye ribarka?
Idan ka zama jakadan haddasa gaba da kiyayya tsakanin Hausa da Fulani meye ribarka?
Kowa ya san Hausawa da Fulani a Nijeriya ba su da gida kamar Arewa. To Arewar, gidanmu, tana cikin matsalolin da ya kamata a ce duk mun tashi mun tsaya muna neman mafita, amma mun tsaya shirme da shiriritar da babu abunda zai kara sai rarrabuwar kai da kara gishiri a tarin matsalolin da suke fuskantar yankin arewa!
Abun kunya ne ma a ce wai wanda suke da dan wayewar kai din da wanda ake tunanin suna da ilmi sune suke sake ruruta wutar kiyayyan!
Kowacce kabila ce kai, in dai kai dan Nijeriya ne matsayinka daya da ko wani dan Nijeriya babu wanda ya fi wani zama dan Nijeriya sai wanda ya fi bada gudumawa wajen cigaban Nijeriya, a aikace, ba a baki ba!
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku