Gwamnan Jigawa, Badaru Na Yi Wa Dan Modi Kafar Ungulu
...Yana amfani da 'yan sanda ana musgunawa 'yan siyasa dake da alaqa da sabon Gwamna mai jiran gado.
Daga Umar Ado Dutse
Tun bayan zabensa a matsayin sabon Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi Dan Modi na samun kalubale mai zafi kala kala daga Gwamnati mai barin gado ta jihar Jigawa karkashin jagorancin Alhaji Badaru Abubakar.
Wasu bayanai na sirri sun tabbatar da cewar tun da farko ba a son ran Gwamna Badaru ne aka zabi mataimakinsa Alhaji Umar Namadi a matsayin dan takara jam'iyyar APC a matsayin wanda zai yiwa jam'iyyar takarar Gwamnan ba, ance wani hamshakin Attajiri ne a jihar ta Jigawa ya tsayawa Dan Modi har ya samu nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC.
Kafin nan an jima ana rade-radin cewar Gwamna Badaru zai yiwa takarar mataimakin nasa yankan baya ta hanyar mara baya ga jam'iyyar hamayya ta PDP, sai dai Gwamnan ya musanta wannan zargi ta hanyar shiga yakin neman zaben Gwamnan jihar wato mataimakinsa Alhaji Umar Namadi Dan Modi.
Sai dai kuma, daga bisani bayan Dan Modi ya lashe zaben Gwamnan jihar, wasu bayanai sun tabbatar mana da cewar Gwamna Badaru tare da wasu majibintansa na yiwa sabon zababben Gwamna kafar ungulu ta hanyar sanya kwamishinan 'yan sanda jihar yana kama da tsare wasu mutanen da suke da alaka da sabon zababben Gwamnan.
Daga cikin mutanan da aka kama wadanda suke da kusanci da sabon Gwamnan akwai tsohon shugaban jam'iyyar APC a jihar Jigawa Alhaji Habibu Sara, wanda zargin alakar dake tsakaninsa da Dan Modi ya sanya Gwamna Badaru Abubakar cire shi daga shugabancin jamiyyar tare da musguna masa ta hanyar sanya 'yan sanda su kama shi.
Haka ma yana daukar nauyin illata su ga kafofin yada labarai da zargin almudahana da kudade don bata suna ko biyan wata bukata.
Yanzu haka dai tsohon shugaban jam'iyyar APC na Jigawa yana hannun jami'an tsaro na yan sanda ba tare da wani laifi ba, saboda bin umurni gwamna Badaru da Kwamishinan yan sanda yake yi.
Baya ga wannan chakwakiyya dake kokari shiga tsakanin Gwamna Badaru mai barin gado da Dan Modi mai jiran gado; akwai zargin da masana tattalin arziki ke yiwa Gwamna Badaru na ci gaba da bayar da kwangiloli da kuma karin kasafin kudi don biyan wasu bukatu ba bisa ka'ida ba.
Zuwa yanzu a cikin abin da bai fi watanni ukku ba, Gwamna Badaru ya sake fasalta kasafin kudi da kashe kusan naira fiye da biliyan biyar na ayyukan da zasu zama nauyi da bashi ga Gwamnati mai zuwa.
Haka ma yana bayar da kwangiloli da ba za a iya samun kudaden biyan su a shekaru hudu masu zuwa ba.
Dama dai ba kasafai ake karewa lafiya tsakanin Gwamna da mataimakinsa ba a irin wannan matsalar ta siyasa.
Sai dai na Gwamna Badaru akwai alamun wata manufa ga sabuwar Gwamnati da ake ganin bai ji dadin kafuwar ta a haka ba.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku