DSS na ci gaba da tsare Baffa Hotoro a Kano

KDK Hausa


DSS na ci gaba da tsare Baffa Hotoro a Kano

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ci gaba da tsare matashin nan Baffa Hotoro bayan ya wallafa bidiyon neman afuwa ga Sheikh ÆŠahiru Usman Bauchi da ya yiwa zagin tsamar nama.

Bayanan da Feedom Radio ta samu sun tabbatar da cewa hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da dama a kan matashin ciki har da na Gwamnatin Kano kan zargin yin kalaman ɓatanci.

Hukumar ta kuma karɓi ƙorafin iyalan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi kan zagin da ya yi masa, kuma shi ne aka kammala yau har ya nemi afuwa.

Nan gaba ne hukumar zata ci gaba da mataki na gaba a kan zarge-zargen da ake yi masa.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku