Hukumar kula da tantance Abinci, Abin Sha da Magunguna a Nigeria wato "National Agency for Food and Drug Administration and Control" ko (NAFDAC) a takaice, ta bayyana cewa Abincin nan na 'kasar Indonesia wato (Indomie) gwamnatin kasar Nigeria bata san dashi ba, NAFDAC sunce dama tun ba yau ba an hana shigo da Indomie Nigeria, musamman Indomie da ake yi daga kasar Taiwan da Indonesia, saboda basu da Rijista da gwamnatin Nigeria.
~ Taiwan da Indonesia dama sune asali suke samar da wannan nau'i na Abinci.
~ Shugabar hukumar NAFDAC ce ta bayyana haka ranar Lahadin Nan, yayin da take amsa tambayoyi daga 'yan Jarida cewa "Shin gaske ne cewa Indomie yana 'dauke da Sinadarin "Ethylene Oxide"?
~ Sai tace "Abu na farko, shi kansa Indomie da ake amfani dashi a Nigeria dama mun haramta shigo dashi tun tuni, saboda basu da Rijista da Nigeria, Indomie da ake yi a Taiwan da Indonesia, ana shigo dasu Nigeria ta barauniyar hanya".
~ "Abu na biyu (Shugabar NAFDAC din tace), Eh tabbas mun samu Complain daga wasu mutane, Masana da masu bincike cewa Indomie yana 'dauke da Sinadarin Nan me guba wajen Saka ciwon Cancer a jikin mutum, wato Sinadarin "Ethylene Oxide", da muka ji haka sai muka zauna a hukumance Kuma muka Saka ranar Talata 2 ga watan May 2023 (Yau kenan) domin kwararru a Nigeria na hukumar NAFDAC zamu fara binciken mu akai".
~ NAFDAC tace, abinda Sakamakon binciken su ya bayyana zasu sanar da kowa da kowa yasan matsayar hukumar game da ci ko amfani da Indomie.
~ Toh sai dai kuma Kamfanin masu samar samar da Indomie a Nigeria sunce Indomie da ake amfani dashi a Nigeria ana yi ne a cikin gida Nigeria, ba daga Indonesia ko Taiwan ake kawowa ba, sunce:
"A tsawon shekaru 25 da muka yi Muna Sarrafa Indomie a Nigeria mun yi Rajista da gwamnatin Nigeria da NAFDAC, kuma wannan Kamfani ne me zaman kansa.
~ "Muna sane da korafin dake yawa akan Indomie, toh amma gaskiya ba Indomie din mu bane na Nigeria, muma mun hada kai da NAFDAC yanzu haka domin gano gaskiya game da wannan Sinadarin Ethylene Oxide da ake rade radin yana cikin Indomien da ake shigowa dashi Nigeria".
~ Sai dai Kamfanonin Indomie a kasar Indonesia da Taiwan sunce sam Indomie da ake producing a 'kasashen su Indomie ne da ya kubuta daga dukkan wata illa ko cuta, sunyi zargin cewa wasu ne dai ke yunkurin bata musu suna".
~ Sai dai a 2022 data gabata gwamnatin kasar Malaysia da take Makwabtaka da Indonesia tayi bincike akan Indomie din, akan samfurin Indomie har guda 36 inda suke tabbatar da tabbas sun gano Sinadarin Ethylene Oxide dake shigar da cutar Cancer jikin mutum.
~ Nan take Gwamnatin kasar Malaysia tayi umarni a cire Indomie din a dukkan shagunan kasar ba sai an jira karewar su ba.
Matakin da Malaysia ta dauka ya fusata kamfanonin Indomie dake Indonesia da Taiwan.
~ Ni dai shawara ta itace, mu hakura da dukkan wani Indomie a yanzu, ga wadanda suke Ci ko amfani dashi, suyi hakuri zuwa lokacin da NAFDAC zata fitar da sakamakon binciken ta.
~ Duk da mun san Allah ne me tsarewa da kariya, amma kada ayi musu ko jayayya da ilimi ko binciken masu bincike, domin abu ne dake alaka da lafiya jama'a, wannan ba abun wasa bane, kuma ana amfani da Indomie din Nan sosai a Kudu da Arewacin kasar nan musamman a tsakanin matasa Maza da Mata, musamman ma Students, 'yan makaranta.
Allah yasa mu dace ya tsare mu...
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku