Ba za ki san zawarci bala'i bane musamman a....

KDK Hausa


Daga: Rasheedah Bintu Abeebakar

Ba za ki san zawarci bala'i bane musamman a wannan karnin namu, sai kin kashe auren ki kin fito nan ne zaki san cewa kin fita daga rahma kin shiga kaiton ki da nadama, sai wancan yazo kina ta murna ga kin samu ɗan fes fes ga kuɗi ga mota, zaizo kamar dagaske auren ki zaiyi sai dai kiji kawai ya fara ce miki kaza da kaza, in kin ci Sa'a kin kuɓuta baiyi lalata dake ya gudu ba, inkuma daman baki da wayo ga kuma kwadayin ki yakai makura daga nan haka wani ma zaizo har a wayi gari kin zamo yar karamar magajiya, ke bari kiji magana ta gaskiya haka ake ta fama. Ga kuma cututtukan da ake ɗauka.

Tun wuri kiyi hakuri da gidan mijin ki ki zauna, matukar ba aikata wani abu yake wanda dole ne ki rabu da shi wanda ya saɓawa Shari'a, inkuma kin fito lallaɓa ki koma in komawar bai haramta ba, inkuma ba halin komawa zauna kiyi ta addu'a ALLAH kawo miki na gari matukar yana da sana'a ga addini lallaɓa ki aure shi, baki san yaushe ne mutuwa za ta riske ki ba yar uwa ta a musulunci.

 Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 



0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku