Mai hali bai barin halinsa
Ƙasar Masar ta maida yan Najeriya sama da 500 su koma Sudan saboda halayyar mutum 2.
Hukumomin ƙasar Masar sun umarci ɗaliban Najeriya sama da 500 su koma ƙasar Sudan biyo bayan gano biyu daga cikinsu ba su da Fasfo ko shaidar tafiya ta gaggawa (ETC).
Wani jami'in Najeriya da ya ɓoye bayanansa ya ce tun farko sun faɗa wa daliban duk wanda ba shi da Fasfo ya jira kaɗan zasu nema masa takardar ETC sannan ya nufi ƙasar Masar.
Sai dai a cewarsa, wasu mutum biyu sun faki ido suka shiga cikin fasinjojin da zasu tafi kuma ba su da fasfo ko ETC, hakan ya fusata mahukuntan ƙasar Masar.
Ya ce a halin yanzun dole sai sun sake dawowa Sudan baki ɗayansu, sun jawo wa sauran tsaikon awanni 10 kuma sai FG ta kara kashe kudaɗe.
Cikakken bayani a ƙasa 👇
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku