Ƴansandan Ghana sun kama ƴan Nijeriya 49 bisa zargin safarar mutane

KDK Hausa



Ƴansanda a Ghana sun kama wasu 'yan Najeriya 49 bisa zargin su da aikaita laifin safarar mutane da kuma laifukan da ake yi ta intanet.

BBC ta rawaito cewa wadanda ake zargin da suka hada da maza 47 da mata biyu an damke su ne a birnin Accra sakamakon rahotonnin leken asiri da aka samu,

'Yan sanda sun yi bayanin cewa guda 45 daga cikinsu wadanda ke tsakanin shekara 18 zuwa 34 da haihuwa an yi safararsu ne zuwa Ghana bayan an yi masu alkawarin aiki kafin aka jefa su cikin aikata laifukan intanet.

Sun kara da cewa an riga an dawo da su Najeriya, ana kuma shirin gurfanar da sauran mutane hudun da ake zargin su ne shugabannin kungiyar a kotu.

Jami'an tsaro sun ce sun samu na'urorin kwamfuta guda 70, da motoci guda biyu, da wayoyin hannu guda 51 a lokacin da suka kai samame gidan wadanda a ke zargin.

Hukumonmi a kudancin kasar sun kai samame irin wannan a wasu bangarorin kasar domin ceto 'yan kasashen waje da dama da ake tsare da su a gidaje daban daban.


Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku