An gurfanar da mutane 3 bisa zargin razana bazawara ta gudu daga unguwar da ta ke a Anambra
An gurfanar da wasu mutane uku, Lazarus Uzor, Anozie Uzor da Valentine Okwuosa a gaban kotun majistare da ke hukunta cin zarafin yara da fyade a Awka, jihar Anambra, bisa zarginsu da yin amfani da asirin rufe fuska wajen tilasta wa wata bazawara mai suna Nneka Uzor guduwa daga unguwar da ta ke a karamar hukumar Ogbaru dake jihar.
An gurfanar da wadanda ake zargin ne a kan tuhume-tuhume biyar a yau Litinin bayan kama su da kwamishinaniyar mata da walwalar jama’a ta jihar Anambra, Ify Obinabo, tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan jihar suka yi.
Sai dai a lokacin da aka karanta kuma aka fassara wa wadanda ake tuhumar laifin, sun musanta aikata dukkan laifukan.
Da ta ke gabatar da bukatar belin wadanda ake kara, babbar alkaliyar kotun, Genevieve Osakwe, ta ce kotu za ta duba bukatar belin wadanda ake tuhuma tunda laifin na beli ne.
An bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan kudi Naira dubu 700 kuma dole ne su bayar da tabbataccen wadanda za su tsaya musu a irin wannan adadin.
Nneka, mai shekaru 53, mai sayar da abinci ce kuma na da ‘ya’ya biyu, dan uwanta, Okwuosa, da wasu su biyu ne su ka kore ta daga cikin al’umma saboda zarginta da ake yi da Naira.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku