Aliyu Betara ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar kakakin majalisar wakilai - APC-Borno

KDK Hausa


Aliyu Betara APC-Borno ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar kakakin majalisar wakilai ta 10 a hukumance, gabanin kaddamar da majalisar a ranar 5 ga watan Yuni.

Betara ya kuma zargi shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila da yin son-rai wajen zaɓen wanda zai gaje shi.

Betara, shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, ya yi wannan magana ne a Abuja a jiya Litinin yayin da ya ke bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin majalisar ta wakilai.

A ranar 8 ga watan Mayu ne kwamitin Æ™oli na jam’iyyar APC na kasa ya fitar da matsaya na shugabancin majalisar zuwa yankin Arewa maso Yamma, yayin da mataimakin shugaban majalisar ya kasance shiyyar Kudu maso Gabas.

A halin da ake ciki, an zabi Abbas Tajudeen (APC-Kaduna) ne domin ya gaji Gbajabiamila a majalisa ta 10, yayin da aka zabi Benjamin Kalu (APC-Abia) a matsayin mataimakin sa

Da ya ke mayar da martani game da wannan matsaya ta jam’iyyar, Betara ya sha alwashin ci gaba ea takararsa.

Ya ce da Gbajabiamila ya zaÉ“i Abass, abin ya bashi mamaki, a lokacin da wasu mambobi da dama suka nuna sha’awarsu na wannan matsayi.

“Idan a yau mataimakin kakakin majalisar ya tsaya takara, shugaban kwamitin kasafin kudi na takara, shugaban masu rinjaye ya tsaya takara, to wane ne ya fi kusa da shugaban majalisar,” in ji shi.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku