Babbar jami'a a cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da ci gaban al'umma ta CITAD Harira Abdurrahman Wakili ta ce babu wata mace da ba ta son aure domin komai lokaci ne.
Harira ta ce, ya kamata maza su cire tsoro su daina cewa matan da ke gwagwarmaya sun fi ƙarfinsu domin hakan rashin adalci ne.
Ta kuma ja hankalin mata masu gwagwarmayar kare haƙƙin mata a Arewacin kasar nan da su fahimci cewa adalci ake nema wa matan ba wai daidaito da maza ba.
Harira Wakili ta bayyana hakan a shirin Fitattun Mata na tashar Freedom Radio kamar yadda zaku gani a wannan link.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku