Abubuwa guda bakwai 7 da zasu sa Mumini ya daina tsoron Kabari.

KDK Hausa




Abubuwa  guda bakwai 7 da zasu sa Mumini ya daina tsoron Kabari.

1. Annabi s,a,w yace: Kabari dausayi ne daga cikin dausayin Aljannah. 

2. Annabi s,a,w yace: Idan aka saka Mumini a cikin kabari, Allah zai cewa Mala'iku: Kuyiwa bawana shimfida daga Aljannah Kuma ku bude Masa kofa daga Aljannah (Inda Rahama zata rika shigowa).

3. Annabi s,a,w yace: Za'a budewa Mumini daga kofofin Aljannah Iskar ta ta rika shigo Masa yana shakar kamshin ta

4. Allah zai yalwatawa Mumini kabarin sa bazai matsa masa kabarin sa ba

5. Za'a sanyawa Mumini kayan 'yan Aljannah bazai zauna cikin likkafanin sa kamar yanda muke zato ba

6. Za'a haskaka kabarin Mumini, bazai kasance a cikin duhu ba

7. Allah zai yiwa Muminai bushara da Aljannah suna a cikin kaburburan su, sai zukatan su su samu nutsuwa sai suyi shauqin a tada alqiyama

YAKU 'YAN UWANA! YAZAMA DOLE MU TACHI MUNEMI ALJANNAH, TAHANYAR YIWA UBANGIJI DA'A. KADA NEMAN WANNAN DUNIYAR YA RUDAR DAMU, DADI NE NA DAN KARAMIN LOKACI

Ya Allah kasa kaburburan mu su siffantu da wadannan siffofin.

Ya Allah kada ka azabtar damu a cikin kaburburan mu


Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku