abubuwa 7 akan rayuwar 'Yan matan yanzu ko mi yasa hakan ?

KDK Hausa


Mu tattauna abubuwa 7 akan rayuwar 'Yan matan yanzu ko mi yasa hakan ?

1- A shekarun baya budurwa bata iya hada Ido hudu da sauryinta a lokacin da suke zance, sai dai ta yi ta satar kallonsa a fakaice sabanin yanzu ?

2- A shekarun baya budurwa ta kan kauracewa unguwar da saurayinta yake ko hanyar gidansu ba ta bi sabanin na yanzu har ziyarar uwar saurayi suke zuwa

3- A shekarun baya budurwa ta kan yi sama da sa sati a gidan miji ba tare da ta fidda hijabi jikinta ba saboda tsananin kunyar namiji da harakar aure sabanin wannan lokaci da tun kafin biki suke watsar da hijabin wasu kuwa tun daren farko 

4- A shekarun baya sabuwar amarya ta kan gudu zuwa makwabta lokacin da za'a kaita gidan miji amma amaren yanzu wasun ma su suke zazzarin a kaisu ko ma su kai kansu wallahi 

5- Lokacin da muna kanana idan ya mace ta hango 'Da namiji zuwa a kan hanyar da take tun daga nesa za ta kauce masa saboda tsoro da girmamawa ga mazan, amma na yanzu har neman bankeka suke subhanallah 

6- A shekarun baya hatta 'Yan yara mata basa yarda su yi wasa da yara maza in ban manta ba har cewa suke " Yan wargi ku tattaro amma banda yan maza" na yanzu har a social Media wasa suke yi da samari, tare da posting din abunda kai ka san duk mace mai kunya ba zata yi hakan ba

7- Na san wayannan kadan ne daga halayen yan matan yanzu wai Dan Allah mi kuke ganin ya haddasa rashin kunyar wasu yan matan kuma minene mafita ?

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku