ABINDA ZAISA ALLAH YA SOKA.
KaÉ—an daga muhadarar da kungiyar Nisa'ussunah Kano state ta shirya a yau talata 16/5/2023 a Masallacin Ihya'ussunah gwammaja.
1. Ka sani cewa ya kai mai imani baza ka samu son Allah ba har sai kaso Allah sannan Allah ya soka.
Ba a baki ake son Allah ba, sai kabi Asbab na son Allah Sannan Allah ya soka, Malama ya kawo asbab guda biyar da in kana aikata su zaka rabauta da son Allah.
A. Bawa ya fifita abinda Allah yake so akan abinda zuciyar sa take so.
b. Ka yawaita ambaton Allah ( duk abinda kake so zaka yawaita ambaton sa)
C. Son Alqur'ani: son Alqur'ani yana cikin son Allah in kana son Allah sai ka luzumunci Alqur'ani domin maganar sa ne.
D. Son masu son Allah alama ce ta son Allah, kaso masu son Allah da Manzon sa.
D. Yin fushi ga wanda ya saɓawa Allah duk wanda ya saɓawa Allah kaji ba daɗi kayi fushi, kaji kai kawai so kake ayiwa Allah biyayya.
2. Jin tsoron Allah da yin Takwa duk wanda yayi Takwa Allah zai soshi
Allah yana son masu takwa.
3.Bawa ya kasance mai yawan tuba Allah yana son bawan sa mai yawan tuba.
4.Bin Manzon Allah (S.A.W) dayi masa É—a'a shima zaisa Allah ya soka.
5. Yin Adalci Allah yana son adalci yana son bayinsa masu adalci.
Akwai ragowar abubuwan da zakayi Allah ya soka guda 20 da Malam ya lissafo Zamu cigaba insha Allahu.
Allah sakawa Malam Sheikh Dr.Ali Yunus Muhammad da alkhairy tare da kungiyar Nisa’us-Sunnah Kano State karkashin jagorancin malama Zainab Ja'afar Mahmud da suka shirya wannan muhadarar mai matukar muhimmanci.
Ya Allah muna rokon ka sonka, da son masu son ka, da son aikin da zai kusanto damu izuwa ga sonka.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku