A sanadin soyayya wasu sun rasa imaninsu,wasu sun rasa mutuncinsu,wasu sun rasa darajarsu,wasu sun rasa lafiyarsu,wasu sun daukaka,wasu sun qasqanta,wasu sun mutu ma gaba daya
Sanadiyyar wasu an juya musu baya,wasu qaddara ta rabasu,wasu suna son maso wani,wasu basu taba tunanin haka ba,wasu sunaso su cire son kuma yaqi fita
Haquri shine maganin mafi yawan matsaloli addu'a da maida al'amari zuwa ga Allah da dangana da kyautatama Allah zato da sadaka da istigfar,suna maida abu mai tsanani zuwa sauqi
Wasu sai suji kamar bazasu sake farin ciki a rayuwa ba,Allah yana sane da kai kuma ba zai baka abinda ba alkhairi bane,komi ya faru yana cikin qaddararka tun asali kuma alqawarin Allah gaskiya ne,idan akayi haquri komi sai ya wuce ya zama labari da yardar Allah
Allah ya sauqaqama duk zuciyar da ke cikin damuwa a so,ya maida damuwarta zuwa farin ciki ya sauya mata da mafi alkhairi.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku