Yanzu haka yan Nageria mazauna sudan suna cikin tashin hankalin....

KDK Hausa


Kira Ga Gwamnatin Nageria Dan Gane Da Mutanan Dake Kasar Sudan Yanzu Hakan.

Daga Real Alameen Minister Yakasai

Yanzu haka yan Nageria mazauna sudan suna cikin tashin hankalin tare da kiran gaggawa zuwa ga gwamnatin Nageria data Yiwa Allah da Manzansa akai musu agajin gaggawa wajan dawo dasu gida Nageria.

Saidai kuma abin ban haushi dakuma takaici irin amsar da gwamnatin Tarayya ta bayar abin Allah Wadai ne dakuma takaici nacewa rashin tsagaita wuta ne yasa har yanzu basu samu damar zuwa ba.

Idan har irin su Amurica,Saudiya, Pakistan, China, Farance, England Zasu iya Shiga su Kwashe yan kasar su mai zaisa Nageria tace bazata iya Shiga ba ita.

Ko a yakin da aka tafka tsakanin kasar Ukraine dakuma Rusian saidai gwamnatin Nageria taji matsin lamba tukunna kafin ta dawo da yan kasarta.

Duk sanda irin Hakan ta faru da yan Nageria mazauna wata kasar zaka cewa sai rai yan kasa ya soma baci tukunna kafin kaga a dau matakin gaggawa.

Hakan yasa ko da yaushe mutane suke kallan cewa da yayan shuwagabannin ne a wannan halin da tuntuni anbi Duk wata hanya da akasan za'abi wajan an kwasosu amma dayake yayan talakawa ne shiyasa gwamnati bata saurin daukar matakin daya dace.

Koma dai menene muna kira da babbar murya ga gwamnati dakuma Duk wanda yake da ruwa da tsaki wajan ganin ankaiwa wayanan mutane agajin gaggawa tunkafin azo ana danasanin da bashi da Wani amfani.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku