Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce ya gayyaci zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da ya kawo ziyara a ranakun 3 da 4 ga watan Mayu domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatinsa ta aiwatar.
Wike ya bayyana hakan ne a jiya Laraba yayin da ya ke duba wasu ayyuka da aka kammala a jihar.
A cewarsa, ayyukan da Tinubu zai kaddamar sun hada da gadar sama ta Rumuola-Rumuokwuta da kuma ginin kotun majistare da ke Port Harcourt.
“mun gode wa Allah. Muna sa ran zaɓaɓɓen shugaban kasa a ranakun 3 da 4 ga wata mai zuwa zai kaddamar da gadar sama ta 12 da ginin kotun Majistare,” inji shi.
“Kuna iya ganin ginin Kotun Majistare da yadda abin yake da ban mamaki. Mun yaba wa dan kwangilar da ya yi wannan aikin, kuma a kan lokaci. Ba na tsammanin za ku iya samun wannan a ko’ina a cikin wannan yanki na kasar.”
Gwamnan ya tuna cewa ya gayyaci ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party da New Nigeria People’s Party, NNPP zuwa jihar don kaddamar da ayyukan da gwamnatinsa ta kammala.
“Mun gayyaci ƴan takarar shugaban kasa na wasu jam’iyyu kamar Labour Party, LP, da New Nigeria Peoples Party, NNPP, duk sun zo sun kaddamar da ayyuka, kuma mun ce masa (zababben shugaban kasa) mun yi imani da cewa bayan zabe, za mu gayyace shi zuwa ƙaddamar da ayyuka. Kuma an yi sa’a an kammala waɗannan muhimman ayyuka guda biyu kafin zuwan nasa,” inji shi.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku