Watarana wani Bawan Allah suna tafiya cikin jirgin ruwa

KDK Hausa


Watarana wani Bawan Allah suna tafiya cikin jirgin ruwa  shi da abokanen shi, sun kai tsakiyar wani teku sai kawai jirgi ya fara tangal tangal, kowa yana ta Æ™oÆ™arin ya samu ya tsira ta hanyar iyo a ruwan domin tsira ammana abun yaci tura saboda zurfin ruwan, sai wannan bawan Allah Ya samu ya maÆ™ale wani kututturen itace, inda shi kaÉ—ai ya tsira..... Saboda yanayi na iska da akeyi, sai wannan kututturen itacen ya kai shi wani tsibiri inda babu mutane ko dabbobi a wajen sai wassu Æ™wari kawai....

Cikin wahala da tashin hankali ya samu ya gina wani tanti da busassun ganyayen bishiya. Ya shafe kwanaki da dama yana kwana a wajen, babu abinda yake samu yaci face ƴaƴan itace. A hankali saboda wahala har ya soma sabawa da wannan yanayin. Har ya fara cire tsammanin ganin dangin shi. Idan dare yayi sai ya samu dutse ya haɗa da wani dutsen yana bugawa har ya ƙesta wuta.....

Watarana da daddare ya Æ™esta wuta kamar yadda ya saba sai ya kwanta bacci. Yana cikin bacci sai kawai yaji hayaÆ™i da zafin wuta sun turnuÆ™e shi, ashe tentin  nashi ne ya kama wuta.... Nan fa ya kama saÉ“o yana cewa: "Haba Ubangiji menene ya sa zaka mini haka, ka kashe Abokai na duka, ka raba ni da dangi nah, ka kawo ni inda babu kowa, gashi yanzu inda nake É“uya É—in ma ka Æ™ona mini shi, gara ae ka kashe ni kawai na gaji da wannan jarabawa haka"...

Gari na wayewa sai ya hangi wani kwale-kwale 🛶 ya nufi inda yake a wannan Tsibirin. Da kwale-kwalen🛶ya tsaya, sai ya nufi wajen matuƙin shi yace: "Captain yaya akayi ka gane ina wajennan?, domin nasan babu kwale-kwalen 🛶 da zaizo wajennan idan ba ɓata ya yi ba"...

Sai captain ɗin yace dashi: "Cikin dare muka hangi wuta, sai muka ɗauka wani jirgin ruwan ne yake ƙonewa, bamu samu mun iso da wuri ba saboda nisan tafiyar dake tsakanin mu da nan, da muka zo sai muka ɗauka kayi amfani ne da wutar domin mu gane inda kake"....

Nan fa mutumin ya durƙusa ƙasa yana kuka yana neman yafiyar Ubangiji akan abinda ya yi na zargin Ubangiji ya cutar dashi ta hanyar ƙona mishi tanti . Nan take ya shiga jirgin ruwan 🛶 suka tafi domin komawa ga iyalen shi da dangin shi...

Ƴan'uwa masu albarka, Ubangiji Ya na da hanyoyi daban daban da Ya kan iya warware mana matsalolin mu. Zaka iya rasa aiki ka ɗauka cewa Ubangiji Ya manta da kai, alhali baka san yana son baka wani aikin sa yafi wanda ka rasa bane. Abokan ka zasu iya rabuwa da kai kada kayi amanna cewa Ubangiji baya tare da kai, yana son ya rabaka da guragurbin Abokai ne. Kada ka zargi Ubangiji komai Kaga Ya yi daidai ne, ba'a tambayar Shi menene Ya sa Ya yi abu, Shi ke tambayar bayin Shi....

 Allah Ya mana jagora 

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku