wani matashi ya kashe kura a Garin Ganye da ke jihar Adamawa

KDK Hausa



Jarumta || wani matashi ya kashe kura a Garin Ganye da ke jihar Adamawa 

A safiyar yau Alhamis ne wanda yazo dai dai da 27 ga watan. Mayu 2023 aka wayi gari da abin mamaki a karamar Ganye dake kudancin jihar Adamawa, inda wani shararren jarumin matashi mai suna Kamkari yayi arangama da kura wacce ta shigo cikin gari inda ya hallaka Kurar har lahira nayan artabu da suka sha:- kamar yadda wakilin Glass 24 ya ruwaito

Awani jawabin da mai martaba Gangwari Ganye Dakta Alhaji. Umaru Adamu Sanda yayi a kofar fadar sa dake tsakiyar garin na Ganye mai mai martaban ya jinjinawa wannan matashin sakamakon namijin kokarin da yayi sannan kuma yayi kira ga matasa suma suyi koyi da abinda Kamkari yayi wurin nuna jarumta hadi da taimakon al'ummar da suke rayuwa acikinta 

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku