Tun Ina matakin firamare ban taba faduwa ba. Har Rana kamar ta yau - Sanata Abdullahi Adamu.
Shugaban Jamiyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, dukkan wata daukaka a siyasa da ake nema hakika Allah ya CIKA masa. Domin tun Yana matakin framare yake jagoranci Kuma shine a sama Bai taba faduwa kasa ba har ranar Mai kamar ta yau.
Adamu ya ce, Hakika Allah ya cika masa dukkan wata ni'ima ta siyasa. Dan haka Yana sanar da Alummar Nasarawa da Najeriya gaba daya cewa, faduwar Dan takarar Sanata a shiyar Nasarawa ta yamma ba faduwa ba ce, nasara ce, a gwada a Gani za'a gane nagari da mugu,
Yaron da ya bukaci a bashi garma ya rike a sake masa har da kotar a Cewar- Sanata Abdullahi Adamu.
Sanata Adamu ya ce, mahaifinsa ya bar masa wasiyya da cewa, a duk lokacin da ya tarar ana fada akan kifi ya rike kan kifin ya bar musu kifin
A Cewar- Sanata Abdullahi Adamu.
Wasu na kallon kaman tsohon sanatan tamkar mayar da martani ne wa zababben sanatan shiyar Nasarawa ta yamma. Ahamad Aliyu Wadada.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku