SULAIMAN AL-RAJHI: Mutumin Da Ya Baiwa Addinin Musulunci Gudummawar Dala Bilyan 16

KDK Hausa



A Bincike kusan a tarihin duniya a yanzu babu wanda ya taba bada irin wannan gudummawar.

A duniyar Musulunci, an dauki Larabawa a matsayin mutanen da suka fi kowa arziki. Suna kashe makudan kudade wajen sayen motoci na alfarma, jirage, kasuwanci da daidai sauransu.

A fadin duniyar nan duk inda zaka ga wani babban kamfani na sayar da da hannun jari, to sai kaga Balaraben mutum a ciki. Dalilin arzikin su kuma shine man fetir da Allah ya azurta su da shi. A kasashen Larabawa ruwa ya fi man fetir tsada.

An haifi Sulaiman Al Rajhi a Al Bukairiyah, a yankin Al Qassim dake kasar Saudiyya. Ya girma a kusa da Saharar Najd inda suka fara gabatar da kasuwancin su da dan uwanshi mai suna Saleh ta hanyar bawa Mahajjata hayar rakumi su gabatar da tafiye-tafiyensu tsakanin Makka zuwa Madina.

A yadda rahoto ya bayyana, Rajhi ya fito daga gida mai arziki, duk da dai cewa shi ma ya sha gwagwarmaya ta kasuwanci, kuma ita ce dalilin da ya sanya ya zama babban dan kasuwa a wannan lokacin.

Sulaiman Abdul Aziz Rajhi yana da kaso mafi yawa na bankin danginsu dake kasar Saudiyya mai suna Al Rajhi Bank.

A shekarar 2012 Rajhi ya karbi lambar yabo daga wajen Sarkin Saudiyya King Faisal, saboda ya bayar da kusan rabin dukiyar da ya mallaka ga addinin Allah, sannan kuma ya bude wani sabon banki na Musulunci da zai dinga taimakon addini.

Kowa dai yasan cewa Larabawa da son nuna kansu a kafafen sadarwa na zamani, sai dai shi kuma Sheikh Sulaiman Al Rajhi na lamarin daban yake da na kowa sai wata hira aka yi da shi a Snap Chat akan yadda ya bayar da sadakar dalar Amurka bilyan sha shida ($16,000,000,000) ga addinin Allah.

Wannan gudummawa da ya bawa addinin Allah dai ita ce mafi girma a tarihi kuma har yanzu ba a sake samun mutumin da ya kama kafar sa ba. Al Rajhi ya bayar da kashi biyu cikin uku na dukiyar da Allah ya ba shi ga addini, inda kuma sauran kashi dayan ya bawa danginsa..


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku