Sarkin Kano Ya Nada Hakimai Hudu, Ya Kara Girma Wasu Shida

KDK Hausa


Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nada Hakimai hudu tare da daukaka matsayin wasu shida.

 Wadanda aka daukaka sun hada da: Malam Umar Sanusi daga Bunun Kano zuwa Dan Makwayon Kano, Malam Hamza Ibrahim Bayero, wanda Dan Madamin Kano ne kuma a yanzu shi ne Danruwata da Malam Lamido Abubakar Bayero wanda aka daga Yarima zuwa Bunun Kano.

 Sauran sun hada da; Alhaji Aminu Ahmad Sadiq daga Zannan Kano zuwa Dan Madamin Kano, Alhaji Magaji Galadima daga Kachallan zuwa Magayakin Kano da Alhaji Habibu Dankadai daga Fagacin zuwa Katikan Kano.

Da yake jawabi ga wadanda aka nada bayan wani biki a fadarsa, Sarkin Kano ya ce an yi nadin ne bisa la’akari da irin gagarumar gudunmawar da wadanda aka nada ke bayarwa wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar.

 Mai Martaba Daraja na Farko ya kara yi musu nasiha da su kasance jakadu nagari na Masarautar Kano tare da yin aiki da sanin yakamata da rikon amana da ikhlasi da tsoron Allah.

 Sarki Aminu Ado Bayero ya kuma nada Alhaji Nura Sunusi a matsayin Dan Darman Kano, Alhaji Sarki Hamidu a matsayin Barayan Kano, Alhaji Sayyadi Mahmud Yola a matsayin Fagacin Kano da Alhaji Belloe Idi a matsayin Kaigaman Kano.


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku