MU LEƘA KANNYWOOD: Zafafan Soyaiya Guda Biyar Acikin Masana'antar Kannywood.

KDK Hausa


MU LEƘA KANNYWOOD: Zafafan Soyaiya Guda Biyar Acikin Masana'antar Kannywood.

Daga: Faisal Sadauki Jos 

1 - FATI WASHA Da Kuma Abokin Aikin Ta ADAM A ZANGO 


     “Fatima Abdullahi Wacce A Ka Fi Sani Da Fati Washa Haifaffiyar Jihar Bauchi Takai Kimanin Shekaru 10 Acikin Kannywood Ta Yi Fina-finai Sosai Amma Wanda Sukafi Tashe Sune, ƳAR TASHA, HISABI, FARIDA Dakuma Shiri Mai Dogon Zango LABARINA, Ƴar Shekara 30 Ɗin Sunyi Soyaiya Sosai Da Babban Jarumin Kannywood Adam A Zango Wacce Suka Kai Kimanin Shekaru 4 Suna Soyaiya Kamar Zasu Auri Juna Amma Hakan Baiyiwu Ba, Daga Ƙarshe Yayi Aure Bai Aure Ta Ba. 

2 - NAFISA ABDULLAHI Da Abokin Aikinta ADAM A ZANGO

 


“Nafisa Abdullahi Haifaffiyar Birnin Jos Jihar Filato Babbar Jaruma Ce A Kannywood Wacce Tayi Fina Finai Sosai Wanda Suka Fi Shahara Sune: SAI WATA RANA, SAFINA, Shiri Mai Dogon Zango LABARINA, Sun Shaƙu Sosai Da Jarumin Nata Adam A Zango Inda Suka Shafe A Ƙalla Shekaru 3 Suna Soyaiya Da Jarumin, Inda Shi Kansa Ya Shaidawa Manema Labarai Cewa “Haƙiƙa Naso Auren Nafisa Amma Allah Ne Baiyi Ba, Kuma Lamarin Aure Sai Allah Yaso”.

3 - FATI MUHAMMED Da Abokin Aikinta ALI NUHU 




“Jarumar Masana'antar Kannywood Fati Muhammad Wacce Takai Tsawo Shekaru 20 Acikin Kannywood, Tayi Fina Finai Sosai Kamar Su: SANGAYA, ZARGE, MARAINIYA, Wacce Ta Auri Sani Mai Iska Shima Jarumin Kannywood Ne Amma Aurensu Ya Mutu Shekaru 3 Da Suka Wuce, "Jarumar Sunyi Matuƙar Shaƙuwa Da Jarumi Ali Nuhu Inda Suka Yi Soyaiya Mai Tsawo Tsakaninsu, Itama Ta Faɗawa Duniya Irin Shaƙuwarsu Da Ali Nuhu Ta Ƙara Da Cewa Aure Nufin Allah Ne Hiyasa Bamuyi Aure Da Jarumin Ba.”

4 - ZAINAB INDOMIE Da Abokin Aikinta ADAM A ZANGO



“Zainab Abdullahi Wacce Aka Fi Sanainta Da Sunan ZAINAB INDOMIE Haifaffiyar Birnin Jos Filato Ne Wacce Tayi Fina Finai Sosai Kamar Su: GARIN MU DA ZAFI, ƳAR AGADEZ, GA DUHU GA HASKE, Labarin Soyaiyarsu Ba Ɓoyaiye Bane Tsakaninsu Da Adam A Zango Ta Aminta Dashi Sosai Farkon Shigar Ta Harkar Film Ɗin Amma Daga Bisani A Shekarar 2014 Zango Yaje Ya Auri Wata Wacce Ba Zainab Ɗinba, Hakan Yasa Ta Shiga Wani Sosai.”

5 - RAKIYA MOUSSA


“Rakiya Moussa Poussi Haifaffiyar Jamhuriyar Nijar Ce Kuma Jaruma Ce A Masana'antar Kannywood Wacce Take Hawa Waƙoƙin Manyan Mawaƙan Hausa Irinsu, UMAR M SHARIFF, GARZALI MIKO, HAMISU BREAKER Dadai Sauransu, Rakiya Ta Nuna Damuwarta Matuƙa Akan Soyaiyar Mawaƙin Da Bata Furta Sunansa Ba Acikin Wani Shirin Da Hadiza Gabon Take Gabatarwa A Shirin GABON'S ROOM, Jarumar Ta Zubar Da Hawaye Akan Soyaiyar Da Take Yiwa Mawaƙin, Inda Tace Har Ta Mutu Bazata Iya Daina Son Sa Ba, Rakiya Tace Zata Iya Zama Dashi Ko Baida Ƙafa Baida Hannu Kuma Makaho Ne Ko Kurma Zata Iya Zama Dashi A Hakan  Hakan Yasa Tausayin Jarumar Ya Shiga Zuƙatan Al'umma Musamman Ƴan Arewacin Najeriya, Wasu Dayawa Sun Danganta Lamarin Da Mawaki Hamisu Yusuf Breaker, Inda Sadauki Yayi Bincike Ya Gano Cewa Sun Daɗe Suna Mu'amala Da Mawaƙin, Saidai Mawaƙin Ya Ƙaryata Lamarin.

          Miye Zakuce ?


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku