NAZARÃ: Matà r Bahaushè Ta Fi Køwace Mace Gata A Dùniya Ammà Ita Cè Ta Fi Gasa Wa Namiji Aya A Hannù
DAGA Zainab Mahmud (Gentle Zee)
A iya binciken da na yi matar Malam Bahaushe tana da gata sosai sama da sauran matan kabilunmu na Nijeriya, domin Malam Bahaushe bai yarda ya ga matarsa ta fita tana aikin karfi ko wahala ba.
Shi duk talaucin sa ya fi so matar sa ta zauna a gida shi ya fita ya yi aikin karfin ko wahalar domin ya nemo musu abin da za su ci shi da ita da yaransu.
Da wuya ka ga matar Malam Bahaushe tana zuwa daukan ruwan da za su sha ko nemo abin da zasu ci, ko daukar nauyin karatunta kø daukar nauyin gidanta da na yaranta ko da kuwa mai hali ce.
Malam Bahaushe idan mai hali ne ma hatta girki da wanki ko wanke-wanke ya haramtawa matarsa sai dai ya dauko masu yi mata hidima. Ita sai dai ta kwanta ta ci ta sha tayi ibada sai kuma kula da tarbiyyar yaransu kawai... Ko Unguwa za ta akwai direba idan ba mota a ba ta kudin a dai daita sahù.
Amma wallahi abin takaici da haushi sai kaji Malam Bahaushe kullum yana kuka da matarsa. Sam ba ta ba shi hadin kai kullum cikin tashin hankali da daga masa hankali take. Da yawa daga cikin ire iren wadannan matsalolin ne kan sa wani namiji qarin aure ko Allah zai sa ya dace ko kuma yayi tunanin tsallakawa ya auro wata kabilar ta daban wacce yake tunanin zai samu zaman lafiya da ita.
Wai kuwa matanmu na qasar hausa suna lura da yadda matan wasu qabilun ke fama da aikin qarfi domin daukar nauyin mazansu da yaransu? Ta dalilin aikin karfin da suke yi har jikinsu ya murde ya zama irin na maza?
Kuma dùk da haka suna girmama mazajensu duk da irin yadda suke gallaza musu kuwa?
Wasu matan kabilun fa su fita kiwon dabbobi ko yin itacen girki, wasu suyi aikin kafinta ko daukar bulo ko gini, wasu da ciki ko goyo suke wannan aikin kuma su samo kudin su dawo gida su girka abinci su ci su da mazajensu da yaransu. Ke kuma matar Malam Bahaushe me ki ka sani game da irin wadannan aiyukan wahalar?
Ni dai wallahi na kasa fahimtar me yake damun wasu daga cikin matan Malam Bahaushe Nè, ko dai dadi ne ya yi musu yawa?
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku