Mai WhatsApp ya kirkiro da fasahar buɗe WhatsApp a wayoyi 4 da lamba ɗaya

KDK Hausa


WhatsApp ya kirkiro da fasahar buɗe WhatsApp a wayoyi 4 da lamba ɗaya 

Fitacciyar manhajar sadarwar nan ta WhatsApp ta saki wata sabuwar fasaha wadda za ta bai wa mutum damar amfani da lamba ɗaya ya buɗe whatsaApp a kan wayoyi daban-daban.

Bayan samar da wannan fasaha, yanzu za a iya amfani da lamba ɗaya a buɗe WhatsApp kan wayoyi har guda huɗu.

Ta yadda za a iya aika saƙo da hoto da bidiyo, kuma zai kasance babu wanda ya isa ya datse shi, (end-to-end encrypted) a kan duka wayoyin.

Idan wayar da lambar WhatsApp ɗin take ta daɗe ba ta aiki, to sauran WhatsApp ɗin duka za su tsaya su daina aiki.

Da wannan sabuwar fasahar, yanzu yadda shiga, da yadda ake fita WhatsApp zai sauya tsari.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku