LABARIN SOYAYYA ❤️: A lokacin da wata budurwa, wata Baiwar Allah taji ta kamu da son Annabi Musa (A.S)

KDK Hausa


Labarin Soyayya❤️:
______________________
A lokacin da wata budurwa, wata Baiwar Allah taji ta kamu da son Annabi Musa (A.S), wato Annabi Musa Bin Imraan, sai taje tace wa Baban ta taga wani mutumin kirki, da ace za'a kira shi a bashi aiki a gidan da hakan ya dace, domin yana da gaskiya, yana da karfin jiki ka karfin ilimi.
قالت إحداهما يا أبت استأجره إن خير من استأجرت القوي الأمين
Sai Baban yace kije ki kira shi, kice ina son ganin sa, tana tafiya tana jin kunya, har Allah yace:
فجاءته إحداهما تمشي على استحياء
Amma wasu yam matan yau kunyar ma basu da ita, idan akwai ma to yar kadan ce, suna tafiya idon su Gar kamar Yar Baby ko Doli ko Teddy.

Sai taje taga Annabi Musa yana zaune karkashin Inuwar wata Bishiya tana hutawa ya gaji, sai tace:
إن أبي يدعوك

Annabi Musa yace Baban ki yana kira na me zai mun?
Sai tace:
 ليجزيك أجر ما سقيت لنا

Daga nan zaka fahimci cewa yarinyar bata saba magana da maza ba, domin data je kawai sai tace Babana yana kiran ka kazo. Bata gaishe da Annabi Musa ba, babu gaisuwa, babu sannu da hutawa, balle karya murya ko murmushin jan hankali.
  ~ Amma ta tabbatar Annabi Musa me gaskiya ne, haka ya kamata da zaran an ganka sau daya toh a gane gaskiyar ka, ta lura da gaskiya sa da amanar sa.
Da wannan zaki fahimci idan kika je kika dauko Layin MTN wato 080 kika kawo gidan ku kika ce wa Baban ku ga wanda kike so, toh kin Kade, a family dinku Zaki zama 081, kece ta farko data kawo shirme.

Sannan wannan Kissar tana nuna Maka cewa ashe Budurwa me hankali tana kokarin nemawa Saurayin ta hanyar samun kudi da taimaka masa ne ba wai ta dinga kwashe masa kudi babu gaira babu dalili ba.
  ~ Domin Annabi Musa bai ce mata yana neman aikin yi ba, itace kawai ta fahimci haka, har tace wa Baban ta ya bashi aikin yi, Baban ya amince.

  ~ Da wannan Qissar zaka fahimci idan yarinya ta samu tarbiyya toh idan ta kawo mutum gidan su da kyar za'a yi nadamar zuwan sa gidan, domin sai ta gama tabbatar da gaskiyar sa da amincin sa kafin ta kawo shi ta nuna shi.
  ~ Samarin mu na yau an tabbatar da gaskiyar su? ko kuma Ado da Kwalliyar su aka tabbatar?

  ~ Annabi Musa yaje wajen Baban ta, ya bashi labarin gaskiyar halin da yake ciki a rayuwa, Allah yace:
فلما جاءه وقص عليه القصص
Da Baban ta yaji halin da Annabi Musa yake ciki a rayuwa na wahala, da rashi, talauci da tsoro, sai yace:
  لا تخف نجوت من القوم الظالمين
Da wannan Ayar zaka fahimci idan ka fadi gaskiya a lokacin da kake neman mace toh Allah zai kawo maka wanda zai tausaya Maka a sha'anin auren.

  ~ Sannan Ayar tana nuna maka cewa, Suruki nagari idan yaji cewa kana cikin wahala ba zai hana ka 'yar sa ba matukan ya yarda da tarbiyyar ka da addinin ka, sannan Siriki nagari yakan mayar da Mijin yarsa matsayin 'dansa, har idan yaga ka shiga damuwa zai ce ka kwantar da hankalin ka, kada kaji tsoro.

  ~ Daga karshe Baban ta yace wa Annabi Musa zan baka auren 'daya daga cikin 'ya'yana biyun nan:
قال إني أريد أن أنكحك إحدى ابنتي هاتين

Amma fa Sharadin auren Yarinyar shine zaka mun aikin Gona da Kiwon Dabbobi na shekaru Takwas (Eight years) ko kuma shekaru 10.
Kaji wani Sadaki fa Allah gafarta Malam 
   ~ Kai zaka iya wannan aikin shekaru 8 ko 10 kafin a baka auren yarinya?

Da wannan zaka fahimci gara ka tsaya ka auri ta gari Koda shekaru zasu yi yawa, akan kayi aure da wuri ka auri 'yar Goma Naira biyu, wato dai maganar da Turawa suke yi cewa:
  ~ It is better to wait long than to marry wrong.

 Baban ta yace, Sadakin 'yata aikin shekaru 8, amma idan ka cika shekaru 10 babu laifi.
على أن تأجرني ثماني حجج فإن أتممت عشراً فمن عندك

Baban ta yace masa, Amma fa don dai Kai ne, shiyasa ban takura Maka ba, na baka Sadaki me Araha da sauki, yace bana so na kuntata Maka:
 وما أريد أن أشق عليك

Baban yace ni kuma zan cika Alkawari ba zan ci Amana ba, in dai kayi wannan aikin na shekaru 8 ko 10 to zan baka Yata, don ni mutumin kirki ne, Dattijo ne ni ba Tsoho ba, bana magana biyu:
  ستجدني إن شاء اللّه من الصالحين

  ~ To haka Dattawa suke, idan suka yi magana basa sauka akai sai da dalili me karfi.
Haka kaima, idan aka yi alkawari da Kai cewa idan kunyi aure zata cigaba da karatu, sai suka dogara da maganar ka suka baka auren, bayan anyi auren sai kace Kai ka Canza magana, ka fasa, ba zata yi karatun ba, wannan ya nuna cewa kai mutumin banza ne.

Annabi Musa yace, babu damuwa, duk wanda nayi a cikin biyun nan (shekaru 8 ko 10 toh ni ba'a cuce ni ba), Malamai suka ce shekaru 10 yayi domin ya girmama Sirikin sa.
  ~ Rashin tarbiyya ne mutum ya baka yarsa amma baka da Wanda kake Wulakantawa sai shi, da wannan Ayar Malamai suka ce idan Baban matar ka yace wane Ina son ganin ka gobe karfe 8 na safe, kace toh, sai Kwatsam ya ganka karfe 7 ko 6, idan yace ai 8 nace kace A'a Baba ai Kiran ka na musamman ne.

  ~ Annabi Musa yace, idan shekaru 8 ko 10 nayi babu wani damuwa, Kuma goman yayi, Allah yace:

قال ذلك بيني وبينك أيما الأجلين قضيت فلا عدوان عليّ واللّه على ما نقول وكيل

Inda zaka tabbatar da cewa Dattijon Nan ya cika alkawari itace Ayar data biyo bayan wannan, Allah yace:
فلما قضى موسى الأجل وسار بأهله آنس من جانب الطور نارا 


Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku