Ku Dora Daga Darrusan Da Kuka Koya A Yayin Watan Ramadan, Sakon Gwamna Bagudu Ga Musulmai
Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu ya yi kira ga musulmai da su dora kan darrusa daban-daban da suka koya a yayin watan Ramadan.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin lakca da aka saba gudanarwa duk watan Ramadan, wanda wannan shine karo na bakwai wanda aka gabatar a dakin taro na masaukin shugaban kasa dake Birnin Kebbi.
Uwargidan Gwamnan Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ita jagoranci Lakcar.
Gwamnan Bagudu, wanda shine shugaban gwamnonin jam'iyyar APC, ya ce kyawawan darrusan da musulmai suka dauka a yayin watan na Ramadan sun hada da yafiya, tausayi, gaskiya, hakuri da sauransu.
Gwamna Bagudu ya kuma yi kira ga musulmai da su yafi juna tare da nuna kauna ga juna. Sannan ya yabawa mai dakinsa, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu kan yadda take hada taron a duk shekara, wanda a cewar sa sakayyar ta na wajen Allah.
A nata bangaren, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, ta bayyana cewa makasudin hada lakcar shine don daukaka addinin musulunci. Ta kuma kara da cewa taron lakcar ta Ramadan ya yi matukar karbuwa a wajen mata, kungiyoyi da dalibai.
Sannan ta yabawa maigidanta kan yadda yake ba ta goyon baya da kuma shawarwari domin samun nasarar taron.
Yayin da take jawabi kan muhimmancin yafiya a musulunci, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ta nemi yafiyar al'umma kasancewar wa'adin mulkin mijin nata ya zo karshe. Ta kuma yi fatan gwamnatin Kauran Gwandu za ta cigaba da gabatar da shirin na Ramadan.
Tun a farko, Gwamna mai jiran gado, Dakta Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya sha alwashin gwamnatinsa ba za ta muzgunawa duk waau masu rike da mukaman siyasa ba. Inda ya kara da cewa zai yi koyi Gwamna mai barin gado, domin a shekaru takwas din da ya yi a kan mulki babu wanda ya muzgunawa illa kokarin hada kan al'ummar jihar da ya yi.
Dr Mufti Menk, Dr Jabir Sani-Maihula, Malama Zainab Jafar Mahmud-Adam da Malama Juwairiya Sulaiman suka gabatar da lakcoci da suka shafi muhimmancin yafiya a musulunci.
Sannan an kuma gudanar da addu'a ta musamman marigayiya Hassana Sule, jami'ar 'yan sanda mai kare lafiyar matar Gwamnan Kebbi da ta rasu sakamakon gajeruwar rashin lafiya.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku