Kasuwancin Yau, daga Hadisan Mai Gidan mu, Annabi Muhammad (S.A.W)

KDK Hausa


Kasuwancin Yau, daga Hadisan Mai Gidan mu, Annabi Muhammad (S.A.W).....
_________________________________
"Ba za ayi tashin Qiyama ba har sai lokaci ya dinga matsowa kusa da kusa, Kuma har sai karya tayi yawa a cikin mutane, Kuma ba za ayi tashin Qiyama ba sai kasuwanni sun matso kusa da kusa".

Annabi Muhammad (S.A.W).
Karanta Musnad na Imamu Ahmad (2/519).

   ~ Zan dauki gaba ta karshe na wannan Hadisin nayi mana takaitaccen bayani akai, gabar da Manzon Allah yace "ba za ayi tashin Qiyama ba har sai kasuwanni sun matso kusa da kusa", saboda akwai abubuwan da zasu 'kara mana Imani da Allah a wannan zamanin idan muka dubi maganar da kuma abubuwan da suke faruwa yanzu.

   ~ Malamai na da dana yanzu sunyi sharhi sosai akan wannan gabar (Allah ya saka musu da alkhairi), daga cikin abubuwan da suka ambata, guda biyar, sai na shida dana ni nake fahimta:.

   1. Ba za ayi tashin Qiyama ba har sai kasuwanni sun matso kusa da kusa, zahirin Hadisin shine kasuwanni za suyi yawa, duk inda ka duba zaka ga kasuwa, anyi kasuwa ko Ina, Masallatai, Asibiti, Gidajen Mai, Makarantu, kan Tituna, cikin Unguwanni da sauran su.
Kasuwa ko branch din kasuwa.

   ~ Saboda akwai wani Hadisin da Manzon Allah yace (Har sai kasuwanni sunyi yawa) ba kamar wannan Hadisin ba da yace (har sai kasuwanni sun matso kusa da kusa), Hadisan suna 'kara fassara junan su kenan, tare da karfafa kowanne.
   Kasuwanni zasu zama basu da nisa da junan su, a wasu wuraren ma kowace Unguwa zaka ga da kasuwar ta, Kuma babba.

   ~ 2. Fassara ta biyu (Ba za ayi tashin Qiyama ba har sai kasuwanni sun matso kusa da kusa), Malamai suka ce hada hadar 'yan kasuwanne zai yi yawa, Wanda yake cin kasuwa 'daya zai koma cin kasuwanni biyu, ko uku, ko bakwai ma.

   ~ Ranar Asabar yana gari kaza, Lahadi yana kaza, har Asabar ta zagayo yana zuwa can da can da nan, kasuwanni basa yi masa nisa, sun matso kusa saboda akwai ababen hawan da zasu Kai shi, ba kamar zamanin daa ba, Wanda har Allah yace suna yin (Rihlatash shita'i was Sayf), a shekara bai wuce Kaci kasuwa 'daya ko biyu, Amma yanzu fa?
Manzon Allah yayi gaskiya (ba za ayi tashin Qiyama ba har sai kasuwanni sun matso kusa da kusa).

   ~ 3. Ma'ana ta uku ta (ba za ayi tashin Qiyama ba har sai kasuwanni sun matso kusa da kusa), abinda ake nufi da kasuwa a nan sune kaya, kayayyaki (Goods) zasu kasance kusa da kusa, kayan da ake samu a Saudiyya zaka gansu birjik a Nigeria, kayan kasar China gasu nan ko ta ina a Nigeria, Made In China, Made in KSA, Made in kaza da kaza.

    ~ Kai kace a kasar ake yi, saboda me kasuwanni, wato kayan suna saurin zuwa.
Kaya (Goods) sai aka kira su da kasuwanni, saboda kaya sune kasuwa ba Rumfa ba, shiyasa aka kira su da kasuwa a Hadisin, kamar yadda wani Mawakin Hausa ya Fadi.

   ~ 4. Fassara ta hudu, ta (Ba za ayi tashin Qiyama ba har sai kasuwanni sun matso kusa da kusa), shine Cinikayya zai matso kusa da kusa, Technological Advancement zai yi yawan da Business din zai sauya, kana zaune a daki kana siyar da Data, kana siyar da Hula, Takalma, Cakes, Samosa.
   ~ Kana zaune zaka yi Order daga kasashen waje, a kawo maka har Kofar gidan ku (Hatta yata Qarabal Aswaaq) ويتقارب الأسواق kenan.
Allahu Akbar, Mai gidan mu kenan, Annabi Muhammad (S.A.W) ya gama bayanin komai over 1,400 years Ago.

   5. Fassara ta biyar na (Ba za ayi tashin Qiyama ba har sai kasuwanni sun matso kusa da kusa), wato harkokin da ada mutane basu dauke su a matsayin harkar kasuwa ba yanzu sun dawo kasuwa, sababbin hanyoyi kasuwanci suna ta bayyana, misali:
   ~ A zamanin da waye yasan harkar Baban Bola, sai daga baya tazo, waye yasan da harkar Wutar lantarki, harkar gyaran Computer, harkar gyaran waya, harkar POS, gyaran Radio, TV, duk sun dawo harkar kasuwa da samun kudi.

   ~ Harkar Gina website da Software development, harkar samar da Mobile Apps, harkar siyar da Recharge card, da Data, Memory card, duk sun bayyana.
   ~ Kai har harkar siyar da wasu abubuwan da baka taba zaton zasu Zama harkar samun kudi ba, misali a yanzu akwai matasan da aikin su shine su nemo Pi Network (Pi dai daka sani Pi din da kake wa dariya) shi suke saya su siyar, dubban mutane sun shiga wannan harkar sosai, suna samun kananna da manyan kudade a harkar Pi, lallai manufar Dr. Nicolas Kokkalis tana ta tabbata slowly a hankali.

Harkar NFT (Non Fungible Token) a duniyar Crypto, da harkar smart contract duk sun bayyana a harkar kasuwa a yau, ana samun manyan kudade da kanan, har ma suna so su kwace hada hadar kudi Mai yawa na duniya ko su jagoranci harkar kudade Mafi girma.

   ~ Wannan Hadisin yana nuna cewa nan gaba Population na duniya zai Kara yawa, domin idan Kasuwanni sukai yawa mutane ne suka fara yin yawa kafin kasuwannin.
Hadisin yana nuna Allah zai Kara yawan Arziki da kudaden da yake baiwa bayin sa, duk da cewa zamani ne da sabon Allah yayi yawa, amma dake Allah mai Rahama ne Arzikin karuwa zai yi, Allahu Akbar.

   6. Na shida:
Haka Kuma, Ina ganin Hadisin zai iya shafan harka Blockchain Technology da Crypto currency, kana rike da Exchanger kwaya daya, Binance, MEXC, Kucoin ko Coin Base, kana hada hadar Tokens da yawa, kasuwa daya ce (Binance) amma ta lullube kananan kasuwanni ana hada hadar CORE, Tron, Matic, BNB, ETH, BTC, Shiba, GMT da sauran su, Kuma a lokaci guda duk kana iya harkar saye da siyarwar su.

   ~ Nace fadin Hadisin yana iya shiga harkar Blockchain Technology, saboda saurin zartas da Transaction (Scalability), maganar da Manzon Allah ya fada na kasuwanni zasu matso kusa da kusa, akwai batun saurin zuwa waje kaza da kaza, toh akan Blockchain cikin second daya mutane Miliyan 5 suna iya saya ko siyarwa.
   ~ Misali, Binance Blockchain yana iya zartas da Transaction dubbai a second daya (Thousands of transaction per second) TPS, kamar kace kyaftawar Ido kenan.

   ~ Blockchain din gargajiya na Bitcoin (BTC) shine ma yake iya zartas da Transaction 17 zuwa 21 a duk second daya, kaga an wuce zamanin wannan saibi da Nawa da wannan.
   ~ Ethereum Blockchain ne ma yake Iya zartas da transactions sama da na Bitcoin per second, Shima dai gargajiyan ne in today's world.

   The lastest and fastest Blockchain to my knowledge shine Bitgert Chain (Braise), wanda yake zartas da transactions sama da dubu Dari uku a Second daya.
    ~ Muna fatan nan gaba a samu Chains din da zasu iya transactions Millions per second, ko CORE ko Pi Blockchain, ko wasu da zasu zo nan gaba. Cikin Second daya mutane Miliyoyi suna iya business a second daya, minti biyu ko minti daya.
ويتقارب الأسواق

Allahu Akbar.
    ~ Wadannan abubuwan duka suna Kara fito da abubuwan da Manzon Allah ya Fada a fili ga wadanda basu fahimtar maganganun sa sai sun ga Technology, ya riga yayi isharan wannan gaggawan ko scalability din tun ba yau ba.

Allah yasa mu dace......

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku