ÆŠan Takaran shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce akwai yiwuwar zababben gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi duba kan cire Sarki Muhammadu Sanusi II, bayan gwamna mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya cire shi daga sarauta.
Hakan na nuni da cewa da yiwuwar dawo da Sarkin na Kano na 14 bisa karagar mulki idan ya karbi ragamar tafiyar da jihar a watan gobe.
Gwamna Ganduje ya tube Sarki Sanusi daga sarautar Kano a ranar 9 ga watan Maris na 2020, inda ya dauke shi zuwa garin Loko da ke Jihar Nasarawa, kana ya nada Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarki tare da kirkiro wasu sabbin masarautu a jihar.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyon da ya karade kafofin sada zumunta, inda yake cewa sun yi iya bakin kokarin su wajen kaucewa sanya baki lokacin da aka tube rawanin Sarki Sanusi da kuma kirkiro sabbin masarautu da gwamnatin jihar tayi.
Tsohon gwamnan Kanon ya ce yanzu dama ta samu saboda haka sabuwar gwamnatin jihar za tayi nazari akan matakin da gwamnati mai barin gado ta dauka da kuma yin abinda ya dace.
Yayin da matakin ya yiwa wasu rai, wasu jama’a sun bayyana damuwarsu akan yadda Ganduje ya warware nadin Sarki Sanusi.
Kwankwaso yace a matsayin su na dattawa zasu ci gaba da baiwa sabuwar gwamnatin Kano mai jiran gado shawarwari na gari akan yadda zata ciyar da jihar gaba.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku