Gobara Ta tashi a Kasuwar Tufafi a Babban Birnin Bangladesh

KDK Hausa

Gobara ta tashi a wata shahararriyar kasuwa ta kayan sawa mara tsada a babban birnin Dhaka, Bangladesh, 4 ga Afrilu, 2023.

  Jami’an kashe gobara na aiki don shawo kan wata gagarumar gobara da ta kone ta wata shahararriyar kasuwar tufafi ta kuma bazu zuwa wasu kananan kasuwanni da gine-gine a babban birnin Bangladesh a ranar Talata. Kawo yanzu dai ba a samu asarar rai ba.

 Gobarar ta tashi ne a kasuwar Bangabazar da ke birnin Dhaka da karfe 6:10 na safe kuma jami’an kashe gobara daga sassa 47 na aikin kashe gobarar, kamar yadda jami’in kashe gobara Rafi Al Faruk ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press ta wayar tarho.

 Ya ci gaba da yin zafi bayan sa'o'i shida da farawa. Anwarul Islam wani jami’in hukumar kashe gobara ya ce kawo yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.
 
 Da yawan masu shaguna a kasuwar Banabazar sun fashe da kuka. Sun kasance suna fatan samun kyakkyawan kasuwanci gabanin bikin babbar Sallah Eid-al Fitr a karshen wannan watan.

 “Ina da shaguna biyu a nan. Komai ya tafi.” Inji Mohammed Mohsin yayin da yake kuka. “An zuba jarina duka a nan. Don me Allah zai hukunta ni haka?"

 ‘Yan kasuwa da dama sun yi kokarin ceto wasu kayayyakinsu amma abin ya ci tura saboda wutar ta bazu cikin sauri.

Ana yawan samun gobara a wuraren kasuwanci a Bangladesh saboda rashin kulawa da rashin tsare-tsaren kare gobara. Sai dai masana'antun tufafin kasar, wadanda suka yi mummunar gobara a baya, sun inganta sosai cikin shekaru goma da suka gabata.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku