Gobara ta kone shaguna 100 a kasuwa a Kaduna
Gobara ta kone kayayyakin na miliyoyin Naira a shaguna 100 da ke shahararriyar kasuwar Yan-Katato da ke karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna, a yau Laraba.
Mohammed Ashiru, Shugaban Kasuwar Yan-Katato, ya shaidawa manema labarai a Zariya cewa gobarar ta faru ne da sanyin safiyar Laraba.
Malam Ashiru ya ce jami’an tsaron kasuwar ne su ka sanar da su cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wata tartsatsin wayar wutar lantarki da ta bi ta saman kasuwar.
"ÆŠigon tartsatsin wutar ne ya haifar da gobarar bayan ya fado kan rufi rumfunan kasuwar kuma daga baya ya kai ga tashin wuta," in ji shi.
Shugaban ya bayyana cewa jami’an tsaron kasuwar ba za su iya kashe gobarar ba, yana mai jaddada cewa sai da jami'an hukumar Kwana-kwana ta tarayya dinka zo sannan su ka kashe wutar bayan ta É—auki awannin ta na ci.
Ya jajanta wa masu shagunan da abin ya shafa, ya kuma umarce su da su dauki lamarin a matsayin ƙaddara.
Jami’in Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya Sabon Gari, DSF Abubakar Ibrahim, ya ce rashin isassun tafkunan ruwa ne ya jawo tsaikon kashe gobarar.
Don haka, ya yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa wa hukumar da rijiyoyin ruwa domin ingantar aikin su.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku