Wata dalibar Jami’ar Jihar Yobe (YSU) Damaturu, Maryam Lawan Goroma, ta rasu jim kadan bayan kammala jarrabawarta.
An tattaro cewa dalibar sashen kimiyyar sinadarai ta fadi a yammacin ranar Alhamis, 27 ga Afrilu, 2023, inda aka garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar da rasuwarta.
Wani abokin karatunsu mai suna Bukar Maisandari, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a shafin sada zumunta na Facebook, ya ce Maryam tana cikin koshin lafiya kafin rasuwarta.
“Innaa Lillaahi Wa Innaa Ilaihir Raaji’uun. Naji a zuciyata na samu labarin rasuwar yar ajinmu Maryam Lawan Goroma. Tana cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali har yau la'asar ta fadi kwatsam aka tabbatar da rasuwarta. Allah Ta'ala Ya gafarta mata kurakuranta. Allah yasa Al-Jannah Firdausi ta zama matabbata ta karshe. Ta'aziyyata ga 'yan uwa da abokanta da duk abokan aikina na Chemical. Allah ya baku ikon jure wannan rashi. Ameen," ya rubuta.
Sai dai wani Abubakar Zaid, ya ce ta yi korafin ciwon ciki a lokacin jarrabawar.
A ranar Juma’a 28 ga watan Afrilu ne za a yi sallar jana’izarta a gidan ‘yan uwa da ke Sabon Fegi a Damaturu.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku