Ba siyasa bace cin zarafin dattijon kirki kamar Farfesa A-A Zuru.

KDK Hausa


Ba siyasa bace cin zarafin dattijon kirki kamar Farfesa A-A Zuru.

Wannan abune na bakin ciki, yadda naga wani Video na rashin hankali da tinani wanda akayiwa Farfesa A.A zuru tsirara a jihar mu adamawa, da nufin aÉ—ebe haushi kan result din da Resident Electoral commissioner na INEC yayi sanarwa a jiya inda ya bayyana abokiyar Gwagwarmaya A'isha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben.

Ga dukkan bayanan da muke samu shine, wannan bawan Allah Farfesa A-A Zuru mutumin ne wanda al'umma dadama sun shedi cewa yana da jajircewa wajan biyayya ga doka da oda, mutun ne wanda ba'a hada kai dashi ayi rashin gaskiya, kamar yadda akai kokarin cutar da al'ummar jahar ta adamawa a jiya.

amman dukda haka saida da akayi hayar 'yan iska, dan su mai wulakanci, bayan sun jibgeshi sannan suka mai tsirara gaban jama'a, kuma aka dora vidiyon suka masa tsirara social media.

Muna rokon Allah ya sakama wannan bawon Allah ga duk mai hannu wurin wannan cin mutunci, da tozarcin da akayi masa, da kuma wulakanta iliminsa da tsufansa da akayi.

Allah ya bimai hakkinsa, Allah ya bashi lafiya, kuma Allah yasa wannan ya zamo silar karin matsayin sa da daukakar sa, a wannan sabuwar gwamnati da muka kafa.

Muna kuma jan hankalin matasa, musamman wadanda akeyo hayarsu dan batawa jahar mu me daraja ta adamawa kima dasu sani cewa, gwamnatin mu bazata lamunci irin wannan rashin da'a ba, kuma lallai muna kira ga mahukunta kan tsaro, dasu gaggauta danko wadannan tsagerun yara dan fuskantar sakamakon hukunci.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku