Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban al’ummar Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayyana ranar Alhamis 20 ga Afrilu, 2023 daidai da 29 ga watan Ramadan 1444 bayan hijira a matsayin karshen azumin watan Ramadan na shekara.
Ma’ana, gobe Juma’a 21 ga Afrilu daidai da 1 ga Shawwal ita ce Idin Alfijir, in ji shi.
Sultan Abubakar, yayin da yake bayyana hakan a fadarsa ranar Alhamis, ya ce an ga watan a sassan Najeriya kuma kwamitin ganin wata na kasa ya tabbatar da ganin watan.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku