An dage horas da masu duba da kididdigar matakin karamar hukumar da aka shirya za a fara gobe

KDK Hausa


SANARWA

 

 Hukumar na son sanar da jama’a cewa an dage horas da masu duba da kididdigar matakin karamar hukumar da aka shirya za a fara gobe 13 ga Afrilu, 2023 saboda wasu matsaloli da suka kunno kai. Za a sanar da sabuwar ranar ga jama'a a lokacin da ya dace.

 Muna tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa Hukumar ta jajirce wajen gudanar da sahihin kuma karbuwar kididdigar yawan jama’a da gidaje a shekarar 2023 kuma duk shirye-shiryen suna kan gaba.

 Don haka muna ba jama’a shawarar su yi watsi da duk wani sako da ya saba wa wannan bayanin. Mun yi nadama kan duk wani rashin jin daɗi da wannan jinkirin zai iya haifar da ma'aikatan.

 

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku