Amma tabbas idan Samari da 'yam mata suka biye ma Chatting....

KDK Hausa


Idan kika biyewa Chatting da Maza Online ba zaki taba tsinana komai a cikin rayuwa ba balle ki tara ilimi ko ki zama wata Baiwar Allah abin alfahari, wancan ya miki message kinyi reply, wannan ya turo a Facebook, wancan a Whatsapp, wancan yayi Text, wancan direct call, wannan Video call, zasu bata miki lokaci ne kawai ki tsufa babu nagarta balle daraja da kima.
   ~ Ke ba koyarwa ko fadakarwa a Online ba, ke ba siyar da komai ba, amma messages sun miki yawa saboda ke Cele ce, ke ake yayi, wallahi ki bayar da shekaru goma masu zuwa nan gaba, babu wanda zai saurare ki a cikin wadanda suke miki messages din nan sai 'yan kadan idan kina da sauran nagarta a lokacin.

   ~ Haka kaima idan ka biye wa Chatting da mata Online babu abinda zaka tsinana a rayuwa a bangaren ilimi, Ibada ko harkar neman kudi da sana'a. Kaga wancan yarinyar kayi mata magana, wancan ka nemi Phone number dinta, kaga wancan kace ta turo maka hoton ta, wancan ka tambaye ta garin su da Unguwar su.
   ~ Haba Malam rejistan National ID Card kake yi ne haka? Ko Tsaban shegantaka ne irin naka?

  ~ Idan mata ka biyewa toh ranar da zaka mutu a Binne ka a Kabari ranar za'a haifi wata da baka taba ganin irin ta ba, ranar da za a Binne ka a Kabari ranar ne wata zata cika cikakkiyar Budurwa kyakkyawa irin wanda kake so.
  ~ Da yawa zaka ga mutane sun wayi gari Idon su yayi ja sun gaji, not because of sunyi Qiyamul Laili cikin dare, saboda sun shafe dare suna chatting ne kawai, haka aka yi jiya, haka kuma za ayi yau.
Wannan yasa zaka ga da yawa basa iya yin Sallar Asubah a jam'i balle akan lokaci, saboda waya ta gajiyar dasu cikin dare.

  ~ Wannan wayar za kayi amfani da ita ne a lokacin da ka san cewa dukkan muhimmai da Farillai na Ubangiji dana rayuwa ka kammala su, ba laifi bane don kana yawan zama online, amma me kake yi online din shine abin tambaya. Akan wannan wayar da zama online mata da yawa sun rasa gane hankalin mazajen su, akan wannan wayar da hawa Online Maza da yawa sun gagara gane gaskiyar matan su.
   ~ Alkhairin dake kan wayar nan ta Android ba kadan bane, amma wallahi sharrin ta abin tsoro ne matuka.

  ~ Karatu yaja baya, ilimi yaja baya, matasan mu babu Fikira, babu dauriya da juriya, saboda duk fasahar ta kare wajen hira da yam mata online, duk basirar ta ya tafi wajen chatting da Maza Online, sai kaga babu wani abin mamaki a kalaman ta, babu wani abin burgewa a tarbiyyar ta da yadda wayewar yazo mata, zaka ga shi kuma babu ilimi a kalaman sa idan yana magana, babu ilimi babu Hikima balle dabara.
  
  ~ Wayar android ta zama one of the strong part of our lives, babu yadda zamu rabu da ita, toh babban aikin shine kada mu yarda ta raba mu da Ubangijin mu, kada ta raba ka da kimar ka da mutuncin ka a wajen Ubangiji da sauran 'yan uwan ka mutane.
   ~ Sana'o'i da yawa sun koma kan Internet, Facebook da sauran su, wani baya da Shago a zahiri amma yana sayar da kayan da ko wanda yake da Shagon Naira Miliyan daya ba zai nuna masa samun kudi ba, 'dakin shine Shagon sa.

  ~ Amma tabbas idan Samari da 'yam mata suka biye ma Chatting a Facebook da Whatsapp at all time zasu fadi babu nauyi a tsakiya da kuma 'karshen rayuwar. Chatting ba laifi bane, zumunci mutunci, har Soyayyar aure ta gaskiya takan shiga, galibin auren yanzu ma haka ne, amma kada ka bari wannan chatting din ya zama shine aims and objectives 'dinka na amfani da Waya ko hawa online.
Allah yasa mu dace.....
✍️
Abdul-Hadee Isah Ibraheem.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku