ADAMAWA FINTIRI YA KAYAR DA BINANI INJI INEC
Hukumar zaɓe INEC ta sanar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Adamawa, wanda ya ƙare cikin Takaddama da sarkakiyya.
Jami'in sanar da sakamakon zaɓen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri'a, 430, 861.
Gwamnan mai ci ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri'a, 398, 788.
Wannan nasara ta bai wa Fintiri ikon ci gaba da mulkin jihar Adamawa a wa'adi na biyu. Kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta tabbatar yau Talata.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku