Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a ranar Lahadi ya bukaci ministan harkokin wajen Rasha da ya saki Evan Gershkovich, wani dan jarida Ba’amurke da ake tsare da shi a makon da ya gabata bisa zarginsa da laifin leken asiri.
Blinken "ya nuna matukar damuwar Amurka game da tsarewar da Rasha ke yi wa wani Ba'amurke ba za a amince da shi ba, kamar yadda wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar wadda ba ta ambaci sunan Gershkovich kai tsaye ba.
Sanarwar ta kara da cewa, a yayin wannan kiran, Blinken ya bukaci Rasha da ta tabbatar da sakin dan jaridar da kuma tsohon sojan ruwa Paul Whelan, wanda kuma ake tsare da shi bisa zargin leken asiri a Rasha.
Wani jami’in Amurka da ya ke magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ce ko da yake sanarwar ba ta ambaci sunan Gershkovich ba, amma shi ne dan jaridar da ake magana.
A karkashin dokar Amurka, ana hana Ma'aikatar Harkokin Wajen yin magana game da wani Ba'amurke sai dai idan mutumin ya sanya hannu kan hana keɓancewa.
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce a lokacin kiran Lavrov ya shaidawa Blinken cewa bai kamata Washington ta sanya siyasa a kamen ba, kuma ta ce kotu za ta tantance makomar Gershkovich, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Ministan ya maimaita ikirari da wasu jami'an Rasha suka yi a makon da ya gabata cewa an kama dan jaridar da "hannu" amma bai bayar da hujjar tabbatar da wannan ikirari ba.
Kiran na Lahadi wani lokaci ne da ba kasafai ake samun tuntubar juna kai tsaye tsakanin Blinken da Lavrov ba, wadanda ba su da hanyar sadarwa ta yau da kullun tun lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine a watan Fabrairun 2022.
Gershkovich, dan jarida na jaridar Wall Street Journal, an tsare shi ne a ranar Laraba a Yekaterinburg, wani birni mai nisan mil 800 daga babban birnin Rasha.
A ranar Juma'a wata kotu a birnin Moscow ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare Gershkovich a gidan yari har zuwa ranar 29 ga watan Mayu. Yana tsare a gidan yarin Lefortovo da ke birnin Moscow.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku