WANI MATASHI A JIHAR BAUCHI YA ZABI AKAI RUWA KAUYEN SU AKAN A BASHI KYAUTAR NAIR MILIYAN SHIIDA

KDK Hausa

WANI MATASHI A JIHAR BAUCHI YA ZABI AKAI RUWA KAUYEN SU AKAN A BASHI KYAUTAR NAIR MILIYAN SHIIDA

Ko kun taba cin Karo da labarin matashi da yayi irin
Wannan Sadaukarwa Irin ta Umar Dan fulani matashi da ya Gwamace a kai ruwa kauyen su akan ya samu kyautar Miliyan Shida ya Gina Kansa. 

GA YANDA ABIN YA FARU 


Wani matashi ya Sanya mutanen sa cikin farin Bayan ya hakura da kyautar Miliyan 6 Daga wani kamfanin da yayi musu aiki. Maimakon tayin tallafin Miliyan Shida da akayi masa ya nemi a samar da ruwa a kauyen su mai suna Sabon Garin kawagga, Gunduman Tulai karamar hukumar Toro jihar Bauchi. 

Matashi wanda akafi sani da Umar dan fulani ya samu aiki da wani company turawa a online mai suna SHIBNOBI , matashin yayi aiki ne da kamfanin Yanda yayi ta kokarin tallata kamfanin a Nijeriya. A Online. 

Ganin kokarin da nayi wajen tallata shibnobi a Nigeria, 
Sai Watara Baban Jami'in Gudanarwa kamfanin tasu
shibnobi mai suna CLIFF FETTNER ya Kira shi yace masa Umar meyene sanar arka, A Nijeriya kaima mu tallafe ka kamar yanda ka tallafa mana? 

Sai Umar yace masa shi Dalibi ne amma Sana'ar da ya keyi shine wankin Motaci kuma da ita ya dauki nauyi karatun sa tun secondary har University, A matsayin sa na maraya. 

Nan take sai Manajan ya masa Albishir cewa an yanke shawaran kamfanin zata Bashi kyautar kudi a Har Naira million 6 kudin Nijeriya Amasayin tallafi, Shima yaje ya karfafa wani aikin sa Domin ya dogara da kan sa a rayuwa A Nijeriya!

Umar yace Ina Jin wannan Albishir din Sai zuciya ta tace min Lallai Miliyan 6 a wajena kudi ne masu yawa wanda zan iya azurta kaina, in taimaki Dangina A matsayi na na maraya. 

Amma ni ina ga lokaci yayi da Nima zan sadaukar Don magance masalar ruwan sha wa kauyen mu wanda muke fama da ita kimanin shekaru 20,

kuma kullum da mu ake neman Wanda zai kawo mana Dauki. Tunda nayi aiki Online kuma Allah ya taimaka na samu Har Miliyan 6 ta hanyar Basira na to wajibi ne Nima na sadaukar Domin na taimaki Al'umma ta.

Umar yace Bayan na yanke wannan shawara Sai na Kira Manajan nace masa in zai yiyu ina son maimako abani kudinnan ,ina son su yi anfani dashi wajen samarwa kauyena ruwan Sha,

Wanda shine matsalar da ta addabi al'umma na kuma ni daya ne cikin mutane da muka shafe tsawon shekaru muna cikin wahalar ruwan Sha,

Wannan Tunani nawa ya baiwa kamfanin makaki Sai da suka yi zama na musamman Suka Girmama wannan shawari nawa kuma
Kai tsaye suka Amince kuma suka Umurceni da in kawo kasafin kudin da za a kashe.
Wajen samar da ruwan 

Cikin yardan Allah na nemi kanfani mai suna BARADEZ NIGERIAN LIMITED, yakawo musu kasafin million takwas( 8)da za a kashe domin samarwa da ishashen ruwan sha a kauyen mu,

Nan take suka Amince suka kara Miliyan biyu cike da yarda da murna sai suka cika sauran kudin, Aka samar mana da ruwan Alhamdu Lillahi Wallahi yanzu Burina yacika mun samu ruwan sha
A kauyen mu kuma ta Dalilina Nagode ma Allah da yayi amfani Dani ya faranta Ran yan kauyen mu inji Umar!!

 SARKIN GARIN KWAGGA SHIMA CIKE DA MURNA YA SHEDA MANA


Da muka tuntubi sarkin kwagga Malam idris kwagga yace babu abinda zamu cewa yaron nan sai dai Sanya masa Albarka da addu'an Allah ya Albarkaci rayuwan sa yanda ya faranta ran mu Shima Allah ya faranta masa nasa fiye da haka.

Sarkin yace A Addinin Muslunci ko Dabba ka shayar Allah zai Shayar da Kai Balle kuma mutane masu yawa haka mungode mungode.

Sarkin ya Kara da cewa wani abin mamaki da Yaron nan mahaifinsa ya rasu, amma da yasamu wannan daman maimakon ya azurta kansa ko ya taimaki yan uwasa sai ya taimkemu gabaki daya, mutanen kauya wanda burin matasa yanzu su samu kudi su manta da kauyensu,

Sarkin ya Kara da cewa ina kira ga Gwannati jihar Bauchi da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafi wanna Yaron ,su bashi aikin yi tunda yagama karatunsa domin samun irin su yana da wahala, kuma wanna abun da yayi yanuna mana idan yasamu mukami zai taimaki mutane, domin ba abun duniya ne agabansa ba.

mun kyautata masa zato kuma shine wakilin mu ko Ina muna masa fatan Alheri irin wannan Yaron kadan ne cikin mutane inji Sarkin.

Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku