![]() |
| Hoton Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin |
Rasha ta kulla yarjejeniya da makwabciyarta Belarus domin sanya makaman kare dangi a yankinta amma ba za ta karya yarjejeniyoyin hana yaduwar makaman nukiliya ba, in ji shugaba Vladimir Putin jiya Asabar.
Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya dade yana tabo batun girke makaman kare dangi a kasar Belarus mai makwabtaka da Poland, kamar yadda Putin ya shaidawa gidan talabijin na kasar.
"Babu wani sabon abu a nan ma, na farko, Amurka ta shafe shekaru da dama tana yin haka. Sun dade suna jibge makamansu na nukiliya a yankin kasashen kawancensu," in ji shi.
"Mun amince da cewa za mu yi haka - ba tare da keta hakkokinmu ba, ina jaddada, ba tare da keta hakkinmu na kasa da kasa kan hana yaduwar makaman nukiliya ba."
Rasha za ta kammala aikin gina wani wurin ajiyar makaman nukiliya a Belarus nan da ranar 1 ga watan Yuli, in ji Putin, ya kara da cewa a zahiri Moscow ba za ta mika ikon mallakar makaman zuwa Minsk ba.
Rasha ta ajiye jiragen sama 10 a kasar Belarus wadanda za su iya daukar makaman nukiliya na dabara, ya kara da cewa tuni Moscow ta mika wa kasar Belarus wasu na'urorin dabarar makami mai linzami na Iskander da za a iya amfani da su wajen harba makaman kare dangi.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku