RIKICIN NA'URAN BVAS INEC TA GARZAYA KOTU BISA TSORON KARTA SAMU CIKAS A ZABEN GWAMNONI
____________
Hukumar ZaÉ“e ta Ƙasa (INEC) ta garzaya Kotun ÆŠauka Ƙara domin neman iznin yi wa na’urorin tantance masu rajistar zaÉ“e (BVAS) garambawul, kafin zaÉ“en ranar 11 ga Maris.
Za a yi zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki jihohi a ranar Asabar, 11 ga Maris.
INEC ta garzaya kotun ne kwana biyu bayan kotu ta bai wa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP iznin binciken na’urorin BVAS waÉ—anda aka yi zaÉ“en shugaban Æ™asa da na majalisar tarayya da su.
Sun nemi iznin ne domin su Æ™ara kafa wa kotun hujjojin da su ke dogaro da su dangane da zargin maguÉ—in da su ke cewa an yi a zaÉ“en ranar 25 ga Fabrairu. Sai dai kuma INEC ta je Kotun ÆŠaukaka Ƙara ta na neman a É—age mata hukuncin hana ta taÉ“a na’urorin BVAS bayan zaÉ“en shugaban Æ™asa.
Kotun ta hana INEC taÉ“a su ne, saboda ta bai wa PDP da LP iznin binciken na’urorin domin su gano zargin maguÉ—in da su ke iÆ™irarin an yi, idan har an yi É—in. Sai dai kuma kwanaki biyu bayan an bai wa su Atiku iznin binciken BVAS, ita ma INEC ta garzaya Kotun ÆŠaukaka Ƙara ta nemi iznin cewa a ba ta damar yi wa na’urorin garambawul saboda da su ne za ta yi aikin tantance masu zaÉ“en ranar 11 ga Maris.
INEC ta ce idan ba ta yi masu garambawul ɗin ba da wuri saboda an ce ta nesance su, tunda an bai wa Atiku da Obi iznin binciken su, to sai dai fa idan ɗage zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki za ta yi.
Ta kafa hujjar cewa ba a Abuja ake aikin yi wa na’urorin garambawul ba, kuma aikin ya na É—aukar Lokaci. Kuma idan ba'ayi ba zai Iya kawo jinkiri kan zaben Gwamnoni dake tafe Domin in ba anyi saiti ba an sake Dora su kan aikin Baza su Iya aikin ba dole Sai anyi garambawul din Wanda dama yana cikin ka'idar aikin su kuma bazai canza komai ba kan sakamakon zabukan inji INEC.
Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku