Mutane Goma Sun Kone A Hadarin Mota A Oyo

KDK Hausa

Adekanye ya ce motocin sun taso ne da wuta inda nan take suka kona mutanen.

 

 Fasinjoji 10 ne suka kone kurmus a wani mummunan hatsari da ya afku a hanyar Oyo zuwa Ogbomoso a ranar Alhamis, 9 ga Maris, 2023.

 Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar, Joshua Adekanye, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Ibadan, ya ce hatsarin ya hada da wata mota kirar Mazda da wata motar bas din fasinja kirar Toyota Hiace, da misalin karfe 5.30 na safe a wajen kilomita 12 a garin Ijawaya. .

 Ya ce motocin bas masu lamba LEM 963 XA da NSR 222 ZS sun fito ne daga jihohin Legas da Nasarawa.

 Adekanye ya ce motocin sun taso ne da wuta inda nan take suka kona mutanen.

 Ya alakanta musabbabin hatsarin da gudu da kuma wuce gona da iri.

 Ya kuma yi kira ga masu ababen hawa da su guji tafiye-tafiyen dare, gudu da wuce gona da iri, ya ce da an rage yawan mace-macen da a ce direbobin ba sa tafiya dare.

Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku