Mutane 10 Sun Kone A Hanyar Oyo-Ogbomoso

KDK Hausa


Daga: Kamil Opeyemi

 Akalla fasinjoji 10 ne suka kone kurmus a hanyar Oyo-Ogbomoso ranar Alhamis.

 An tattaro cewa, fasinjojin da suka yi taho-mu-gama da suka hada da Mazda da kuma motocin fasinja kirar Toyota Hiace, sun kone kurmus ba tare da an gane su ba.

 Hukumar kiyaye hadurra ta tarayya ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Alhamis a Ibadan.

 Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar, Joshua Adekanye, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 5.30 na safe daura da Kilomita 12 Ijawaya kan hanyar Oyo-Ogbomoso.

 Ya ce motocin bas masu lamba LEM 963 XA da NSR 222 ZS sun fito ne daga jihohin Legas da Nasarawa.

 Adekanye ya ce motocin sun ci wuta nan take wanda ya yi sanadin kona mutanen.

 Ya alakanta musabbabin hatsarin da gudu da kuma lodi fiye da kima.

 Ya kuma yi kira ga masu ababen hawa da su guji tafiye-tafiye da daddare, da gudu da kuma wuce gona da iri, inda ya ce da an samu raguwar mace-macen idan direbobin ba sa tafiya dare.

Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

KDK Hausa 

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku