Matashi ya halaka abokin takarar sa a wajen budurwa a Madagali Jihar Adamawa.

KDK Hausa

Matashi ya halaka abokin takarar sa a wajen budurwa a Madagali Jihar Adamawa.

Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke wani matashi mai shekara 22 a duniya, mai suna Muhammad Bala, wanda ya fito daga Mararaban-Madagali cikin ƙaramar hukumar Madagali, bisa zargin halaka wani abokin takarar sa.

Ana zargin Muhammad Bala da halaka wani matashi mai suna Bakura, wanda suke neman wata budurwa da niyyar aure tare Majiyar GRTV ta ruwaito.

Wanda ake zargin dai ya aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Fabrairun 2023, da misalin ƙarfe tara na dare a gidan su budurwar mai suna Maryam Muhammad bayan zazzafar gardama ta ɓarke a tsakanin su.

Lokacin da ƴan sanda ke tuhumar sa, wanda ake zargin ya bayyana cewa da shi da abokin takarar ta sa sun sha samun saɓani a baya sannan sun ja kunnen junan su kan su daina zuwa wajen Maryam.

An samo cewa ranar da lamarin ya auku, matasan biyu sun haɗu a gidan su yarinyar inda rigima ta ɓarke a tsakanin su.

Rigimar ta rikiɗe ta koms faɗa, wanda ana cikin hakan kawai sai wanda ake zargin ya cakawa marigayin wuƙa wanda ya rasu daga raunikan da ya samu.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar Æ´an sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, yace za a tura wanda ake zargin zuwa kotu da zarar sun kammala bincike.

Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku