BANBANCIN MATAN DA DANA YANZU
Matar auren da da wuya ta dubi idon mijinta tace "Ina son ka" amma a kullum zatayi abinda zai qara qarfin qaunarta a zuciyarsa,tana girmamashi matsayinsa na jagoranta,tana boye aibinsa ta bayyana alkhairinsa duk sabanin da zasu samu da wuya kaga tayi wani abu wai shi "yaji"inji hausawa.
Idan Allah yasa mai rufin asiri ne yana da wadata zata tayashi killace kayansa zata zama abokiyarsa a komai nasa cikin girmamawa da kulawa,idan kuwa Allah ya sa mai qaramin qarfi ne itace farkon boye talaucinsu da tayashi neman yadda zasu rufawa juna asiri,wata ko iyayenta bazasu san halin da take ciki ba.
Idan tanada abokiyar zama zaka samesu tamkar 'yan uwan juna babba zata ja girmanta har qarama tana kiranta da " ya ya"zasu taimakawa mijinsu wajen samun aljannarsu gaba daya 'ya'yayensu duk kansu a hade,in daya batanan daya zata iya cigaba da tarbiyyarsu kamar nata.
Duk da ba karatu garesu sosai ba,amma suna qoqarin aiki da duk ilimin da Allah ya sa suka samu,basa iya fadar sunan mijinsu ko a bayan idonsa,basa sa insa da mazajensu,basa yawace yawacen da bai kamata ba,mafi yawancinsu zaman aure yafi su fita aiki ko wata sana'a daba a gida za'a yita ba.
Matar da butar mijinta daban kujerarsa daban,maficinsa daban,tabarmarsa daban,kwanon abincinsa daban,iyayenta ta daukesu tamkar nata 'yan uwansa ma haka,zata iya shekara bata fita daga gidan mijinta inba da kwakkwaran dalili ba, Shiyasa suka sami rayuwa mai kyau,da soyayya da aminci a tsakaninsu,ya'yayensu sukayi albarka rayuwarsu ta inganta,farin cikinsu ya yawaita.
Yawancinsu an aurensu tun basu mallaki hankalin kansu ba,da tarbiyyar mazajensu sukeyin wayo,shi yasa suke matuqar girmamasu,basu damu kansu da dukiyar miji kamar farin cikin mazajensu ba.
Da yawansu ko fuskar mazajen basu sani ba,sai bayan an kaisu dakinsu,shiyasa basuyi wayon da har zasuce sai miji kaza ko mai kaza zan aura ba. Kadan kenan daga banbancinmu dasu shiyasa suka fimi samun albarka farin ciki da nutsuwa.
Allah yasa mu dace .
Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku